Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Tasa Keyar Bakin Haure 135 Zuwa Costa Rica


Wasu ‘yan kasar Costa Rica da Amurka ta mayar kasarsu
Wasu ‘yan kasar Costa Rica da Amurka ta mayar kasarsu

Jirgin saman da ya daukesu ya tashi ne daga garin San Diego, na jihar California, inda ya sauka a wani sansani dake kusa da tashar jiragen saman kasa da kasa ta Juan Santamaria.

Amurka ta tasa keyar bakin haure 135 daga kasashe daban-daban, ciki harda yara kanana 65, zuwa kasar Costa Rica a jiya Alhamis, a cewar gwamnatin Costa Rican.

Jirgin saman da ya daukesu ya tashi ne daga garin San Diego, na jihar California, inda ya sauka a wani sansani dake kusa da tashar jiragen saman kasa da kasa ta Juan Santamaria, kamar yadda kamfanin dillancin labaran AFP ya tabbatar.

An yi safarar bakin hauren, wadanda za’a mayar zuwa kasashensu na asali daga Costa Rica, a cikin motar safa daga babban kasar San Jose zuwa wani sansanin yan gudun hijira da ke da tazarar kilomita 360, kusa da kan iyakar kasar da Panama.

Dukkanin yara 65 dake cikin jirgin sun samu rakiyar wani danginsu, a cewar mataimakin ministan harkokin cikin gidan Costa Rica Omer Badilla kuma babu ko mutun guda daga cikin wadanda ke cikin jirgin dake da tarihin aikata laifi.

Bakin hauren sun hada ‘ya’yan kasashen Afghanistan da China da Iran da Rasha da Armenia da Georgia da Vietnam da Jordan da Kazakhstan da kuma Ghana.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG