Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawan Najeriya Ta Gayyaci Manyan Jami'an Tsaro Kan Zargin USAID Na Daukar Nauyin Boko Haram


Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher Gabwin Musa
Babban Hafsan Tsaron Najeriya Janar Christopher Gabwin Musa

Majalisar Dattawa ta dauki haramar yin bincike kan zargin da dan Majalisar Dokokin Amurka, Scott Perry, ya yi cewa Hukumar Gwamnatin Amurka mai Tallafa wa Kasashen Duniya, USAID, ita ce ta rika tallafa wa Kungiyar Boko Haram a Najeriya.

Wannan yunkuri ya biyo bayan kudurin da Sanata Mai wakiltar Jihar Borno ta Kudu, Mohammed Ali Ndume, ya kawo zauren Majalisar a zaman su na jiya laraba kuma Majalisar ta amince da bukatun Ali Ndume kamar.

Majalisar ta gaiyyaci manyan jami'an tsaro da suka hada da mai ba shugaban kasa shawara kan harkar tsaro Nuhu Ribadu da Darekta Janar na Hukumar leken asirin kasa da Ma'aikatar harkokin Wajen kasar domin gabatar da wani jawabi na gaggawa kan zargin da aka yi cewa Hukumar USAID ke tallafa wa Boko Haram a Najeriya,

Wannan mataki ya biyo bayan kudurin da Sanata Mohammed Ali Ndume ya gabatar, wanda ya bayyana wani faifan bidiyo na dan Majalisar dokokin Amurka ,Scott Perry, yana zargin Hukumar USAID ta na tallafa wa Kungiyoyin ta'addanci ciki har da Boko Haram. Sanata Mohammed Ali Ndume ya yi ma Sashen Hausa karin haske kan Kudurin gaggawa da ya gabatar gaban Majalisar inda ya ce kowane dan Najeriya na fatan ganin Majalisa ta dauki mataki kan wannan zargi ganin cewa dabi'un kungiyar Boko Haram a shekarun bayan na nuna cewa suna samun tallafi daga wani waje wanda ba a sani ba. Ndume ya ce biri ya yi kama da mutum domin Boko Haram ba su da filin jirgin sama na su, ba su da tashar tekun ruwa na su amma kuma irin kayan aiki da suke da shi yana ba wa mutane mamakin inda suke samowa. Ndume ya ce ana ta samun bayanai daga mutane masu gani da ido cewa su kan ga ana sauke wa wasu mutane kaya daga jirgin sama mai saukar angulu a cikin daji da dare, saboda haka dole ne a yi wannan bincike domin zargin ya fito ne daga zauren Majalisar Amurka. Ndume ya kuma tunatar da cewa Gwamnati Tarrayya a tsawon shekaru tana kokarin samar da matakan dakile ayyukan Kungiyoyin ta'addanci a kasar inda har ya bada misali da korafin da babban hafsan Sojojin Najeriya, Janar Christopher Gwabin Musa, ya yi cewa Kungiyoyin Kasa da kasa ne ke daukar nauyin kungiyoyin ta'addancin Boko Haram tare da horar da su tunda ba sa yarda a sa ido a harkokin su.

A nashi nazarin, masanin harkokin tsaro, Dokta Kabir Adamu, ya nuna cewa wannan mataki da majalisa ta ce za ta dauka na gayyatar shugabannin hukumomin tsaro ba daidai ba ne. Kabir ya ce wannan ya nuna cewa ba su san aikinsu ba, domin bangaren Majalisar Dattawa ta Najeriya tana da damar aika wa Majalisar Amurka cewa tana son a ba ta sakamakon binciken, ba sai ta nemi yin wani zama na sirri ba. Kabir ya ce wannan ne abubuwan da ke bata wa Majalisar suna, tunda su ne suke sa ido da bibiya kan wadannan abubuwa da aka yi zargi, kuma ba ta yi aikinta ba. Kabir ya ce ba shugabannin hukumomin tsaro ya kamata Majalisa ta kira ba, ya kamata Majalisa ta kira Ma'aikatar Kasafin Kudi da tsare tsare ne domin su ne masu sa hannu na yarjejeniya tsakanin kasar da Hukumomin Kasa da Kasa irin su USAID din.

Abin jira a gani shi ne ko binciken da majalisar dattawa za ta yi a cikin sirri, zai haifar wa kasar da mai ido.

Saurari cikakken rahoton Madina Dauda:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG