Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Wakilai Ta Bukaci Gudanar Da Binciken Gaggawa Akan Ma’aikatan Tashoshin Jiragen Saman Najeriya, Tayi Sammacin Keyamo

Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)
Zauren Majalisar Wakilan Najeriya (Facebook/House of Reps, Nigeria)

Yayin da take gabatar da kudirin mai matukar mahimmanci ga kasa, majalisar ta bukaci Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ya gudanar da cikakken bincike akan ma’aikatan dake aiki a tashoshin jiragen saman najeriya.

Majalisar Wakilan Najeriya ta bukaci gaggauta gudanar da cikakken bincike akan ma’aikatan tashoshin jiragen saman kasar.

Dan Majalisa Jesse Onuakalusi ne ya gabatar da kudirin gaggawar mai matukar mahimmanci ga kasa, a yayin zaman majalisar na yau talata.

‘Yan Majalisar Wakilan sun kuma bayyana damuwa akan matakan kiyaye afkuwar hadura a tashoshin jiragen saman Najeriya, sakamakon zargin daukar ma’aikatan da basu da kwarewa aiki.

Yayin da take gabatar da kudirin mai matukar mahimmanci ga kasa, majalisar ta bukaci Ministan Sufurin Jiragen Sama, Festus Keyamo ya gudanar da cikakken bincike akan ma’aikatan dake aiki a tashoshin jiragen saman najeriya.

Haka nan kuma majalisar ta bukaci a gudanar da bincike akan dukkanin ‘yan kwangilar da aka baiwa aiki a tashoshin jiragen saman a shekarar data gabata.

Daya daga cikin shawarwarin da aka cimma yayin zaman majalisar sun hada da, gayyatar Keyamo ya bayyana gaban Kwamitin Majalisar akan Sufurin Jiragen sama nan da kwanaki 7.

Hakan na zuwa bayan da Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Saman Burtaniya, ta kai rahoton rashin yin biyayya ga ka’idojin kiyaye afkuwar hadura ga takwararta ta Najeriya, NCAA, akan daya daga cikin kamfanonin jiragen saman Najeriya mai suna “Air Peace”.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG