Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, ya gana da shugaban Najeriya Bola Tinubu a yau Talata a fadar gwamnati dake Abuja babban birnin tarayyar Najeriya.
A talatar nan ne, malaman firamare a babban birnin tarayyar Najeriya, suka gudanar da zanga-zanga a dandalin “Unity Fountain” dake Abuja.
Majalisar Dokokin Jihar Ogun ta tsige Shugabanta, Kunle Oluomo, daga kan mukaminsa.
Gwamnatin jahar Filato ta sanya dokar hana yawo na awoyi ishirin da hudu a karamar hukumar Mangun jihar Filato.
Rundunar ‘Yan Sandan jihar Neja ta tabbatar da ceto hudu daga cikin mutane 17 da ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su daga dajin Kpakuru da ke garin Kagarko a jihar Kaduna da kuma kauyen Chachi na karamar hukumar Tafa.
Gamayyar Kungiyoyin Arewa Ta Kira Taron Gaggawa a Abuja game da matsalar tsaro.
Mai shari’a James Omotosho na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya soke kasafin Naira biliyan 800 da kungiyar ‘yan majalisar dokokin jihar Ribas karkashin jagorancin Edison Ehie ta amince da shi da kuma sanya hannun gwamnan jihar Ribas, Siminalayi Fubara.
Shugaban kasar Amurka Joe Biden, ya bayar da takardar shedar karramawa ga tsohuwar jami’ar sojin saman Amurka, Sarauniya Irene Olasumbo Cole, ‘yar asalin Najeriya, domin sadaukar da kai da ta yi wajen yi wa kasa hidima a rundunar sojin kasar Amurka.
Hajiya Inna Galadima ta jam'iyyar APC, ta zama zababbiyar shugabar karamar hukumar Jere ta jihar Borno, ta kasance Shugabar Karamar Hukuma mace ta farko a jihar.
Gwamnatin jihar Legas a Najeriya ta rufe kasuwar Oke-Afa, Isolo, da Katangua, Abule Egba, bisa karya ka’idojin zubar da shara, da suka hada da rashin tsaftar muhalli a kasuwannin, wadanda ke haifar da munanan laifuka na muhalli.
“Muna muku godiya saboda labaru masu inganci da kuke ba mu, wannan gidan rediyo naku yana da babban aminci. Gidan rediyo ne da kasashenmu na Afirka suke amfani da shi.” Shugaban kungiyar kare hakkin dan adam ta CODDAE a Nijar, Alhaji Moustapha Kadi.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.