Dan wasan Equatorial Guinea Ivan Salvador ne ya fara zura kwallo a ragar Najeriya a minti na 36
Najeriya na rukunin 'A,' mai dauke da Ivory Coast, Guinea-Bissau da kuma Equatorial Guinea.
Kotun kolin Najeriya ta yi watsi da hukuncin Kotun Daukaka Kara da na Kotun Sauraron Kararrakin Zaben gwamna da suka tube dan takarar jam’iyyar NNPP Abba Kabir Yusuf tare da tabbatar da shi a matsayin gwamnan jihar Kano.
Tawagar masu shari’ar mai mambobi biyar a hukuncin da aka yanke na bai daya da Mai Shari’a Lawal Garba ya yanke, sun tabbatar Babajide Sanwo Olu a matsayin wanda ya lashe zaben da aka yi a ranar 18 ga Maris, 2023, bayan da suka yi watsi da kararraki guda biyu da ke kalubalantar nasarar sa.
A wani gagarumin mataki don tabbatar da samar da inganci a fannin hada-hadar kudi a Najeriya, babban bankin kasar wato CBN ta sanar da rusa hukumar gudanarwar bankin Union, bankin Keystone, da bankin Polaris.
Hukumar Alhazai ta kasa NAHCON ta bukaci bankin cigaban Musulunci da ya baiwa Najeriya damar shiga kasuwannin Saudiyya na cinikayya da hada-hadar sayen dabbobin da ake amfani da su a lokacin ibada na aikin Hajji.
Mai Shari’a Jude Onwuegbuzie na babbar kotun babban birnin tarayyar Najeriya dake zamanta a unguwar Apo, ya bada belin tsohon Ministan Lantarki da Karafa na kasar, Olu Agunloye, akan kudi naira milyan 50.
Kotun Kolin Najeriya da ke zamanta A babban birnintarayya, Abuja, za ta yanke hukunci kan kararrakin gwamnoni bakwai a ranar Juma’a, 12 ga Janairu, 2024, wanda zai fara da karfe 9 na safe.
Shugaban Kasar Najeriya Bola Tinubu ya nuna alhininsa bisa rasuwar Sheikh Abdul-Hafeez Aṣhamu Abou, Baba Adinni na Legas, wanda kuma shi ne Shugaban Majalisar Zartarwa na Babban Masallacin Legas.
Kotun koli dake da zamanta a birnin tarayyar Najeriya, Abuja, ta tabbatar da Umo Eno na jam’iyyar PDP a matsayin zababben gwamnan jihar Akwa Ibom bayan ta yi watsi da karar da jam’iyyu uku suka shigar na kalubalantar sakamakon zaben da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris na shekarar 2023.
Yayin da gwamnatin Najeriya ke cewa tana daukar matakai domin bunkasa ayukkan kasuwanci da habaka tattalin arziki, wasu 'yan kasuwa na kokawa akan cewa har yanzu suna fuskantar kalubale da ke yin tarnaki ga kasuwanci da kuma tattalin arzikinsu.
Attajirin dan kasuwa, Aliko Dangote, ya kwato matsayinsa na attajirin da ya fi kowa arziki a nahiyar Afirka, kamar yadda mujallar Forbes ta bayyana.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.