WASHINGTON, D. C. -Takardar karramawar, wadda Shugaba Biden ya sanya wa hannu da kansa na cewa: “Amurka ta karrama marigayiya Irene O. Cole. Ana mika wannan ne daga al’umma da ke cike da godiya, domin bayar da sadaukar da kai a hidimar kasarmu a aikin Rundunar Sojojin Amurka.”
An haifi marigayiya Irene Cole ne a jihar Legas ga iyalin Thomas Cole. Ita jikanyar Hezekiah Oladipupo Davies ce. Ta girma a karkashin kulawar Mama Olufumilayo Anikulapo Kuti kuma ta shahara a autocorrection.cancel da ta lashe wata gasar “Miss Legs” wato wadda ta fi kyaun kafafu, kuma ita ce mace daya tilo a Najeriya da ta taba lashe wannan gasar ta “Miss Legs”.
Haka kuma an tabbatar da hakan a cikin wata sanarwa daga abokanta a Amurka wadda Florence Carter ta wakilta tare da mataimakiyarta ta musamman a Najeriya, Christian Amariwu
Suke ce: “Babbar zakanya, muryar wandanda aka zalunta, mai ba da shawara ga marasa murya, mara tsoro, yau cika shekara guda da mutuwar ki. Amurka da duk duniya suna bankwana da babbar jaruma. Allah ji kanki.”
Dandalin Mu Tattauna