WASHINGTON, D. C. - Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun darakta mai kula da harkokin jama’a na hukumar kula da shara ta Legas, Misis Folashade Kadiri. LAWMA ta ce rufe kasuwannin ya zama dole don dakile karuwar matsalolin kiwon lafiya da muhalli.
Da yake tsokaci game da ci gaban, kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa na jihar, Mr. Tokunbo Wahab, ya ce wani shirin gwamnati a bara da bai lamunci zubar da shara ko’ina ba yana nan daram, don haka gwamnatin jihar Legas ta haramta amfani da rarraba robobin rike sanyi ko zafi da ake amfani da su don sau daya a jihar.
Kwamishinan muhalli da albarkatun ruwa, Tokunbo Wahab, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Lahadin da ta gabata ta hannun Daraktan hulda da jama’a na ma’aikatar, Kunle Adeshina.
Ya kara da cewa, robobin rike sanyi ko zafi ne ke da babban kaso na sharar da Hukumar Kula da Sharar ta Jihar Legas ke mu’amala da su akai-akai da ake zubar wa akan manyan tituna da kasuwanni.
Adeshina ya yi nuni da cewa, ya kamata hukumar Yaki Da Rashin Da’a da hukumar kula da sharar ta jihar su dakatar da ayyukan duk wani kamfani da ke kera robobin da kuma kamfanonin rarrabawa da ke cikin jihar domin kaucewa ci gaba da rabawa.
Dandalin Mu Tattauna