Gwamnatin Tarayya na dab da fara aiwatar da shirinta na tillastawa hukumomi da ma’aikatun gwamnati ware kaso 5 cikin 100 na guraben aikin yi ga masu bukata ta musamman a fadin Najeriya.
Wasu sarakuna da suka hada da 'yan majalisar Sarkin musulmi na dakon fuskantar hukunci, sakamakon wani kwamiti da gwamnatin Sakkwato ta kafa don gudanar da bincike akan zarginsu da aikata laifuka masu alaka da siyasa.
Sama da kwanaki 100 da sace daliban Jami’ar Gwamnatin Tarayya dake Gusau na jihar Zamfara, iyayen yaran sun sake kaiwa gwamnati kokensu don ta kara kaimi wajen biyan bukatun da ‘yan ta’addan suka gabatar na musayar mutanensu dake tsare a hannun gwamnati da ‘ya’yansu.
A lokaci kadan daga yanzu Kotun Kolin Najeriya, wacce ita ce ta karshe za ta yanke hukuncin zaben gwamnonin jihohin Kano, Zamfara, Nasarawa da Filato.
Tsohuwar ministar dai tun makon da ya gabata ne ya kamata ta bayyana a ofishin na EFCC, amma dai bisa rahoton da jaridun cikin gida na Najeriya sun bayyana cewa tsohuwar ministar bata sami zuwa ba.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya dakatar da Ministar agaji da Walwalar Jama'a, Betta Edu nan take.
Shugaban gwamnonin arewacin Najeriya Muhammadu Inuwa Yahaya ya bayyana cewa, an mance da aikin tono danyen man fetur a Arewacin Najeriya bayan kaddamar da rijiyoyin fetur na Kolmani a Gombe da Bauchi.
Kungiyoyin dai sun yi kira da a hukunta duk wanda aka samu da hannu cikin lamarin domin ya zama izina ga wasu.
Kungiyar tuntuba ta dattawan Arewa ACF, ta koka kan yadda ba’a zartar da hukuncin da ya kamata kan mutanen da ke da hannu akan matsalolin satar yara da akan yi safarar su daga yankin arewacin Najeriya zuwa kudanci domin sayar da su.
Kamfanin na Dangote ya kara da cewa har ya turawa EFCC wasu bayanai a mataki na farko, amma jami’an hukumar suka ki karbar bayanan suka kuma matsa cewa sai sun kai ziyara hedkwatar kamfanin.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.