Bayanai na nuni da cewa hakan na faruwa ne yayin da matsalar ta rashin tsaro ke raguwa a arewa maso yammcin kasar, kamar a yankunan jihar Sokoto.
Za ta kafa tarihi a watan Mayu, bayan da abokan aikinta baki danayansu suka zabe ta a matsayin Magajiyar garin Leeds a Burtaniya.
Kotun koli ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna karkashin inuwar jam’iyyar PDP, David Umbugadu ya shigar kan nasarar gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa a yau Juma’ah.
Kotun koli ta yi watsi da karar da dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP, Isah Ashiru ya shigar na kalubalantar nasarar gwamna Uba Sani na jihar Kaduna a zaben shekarar 2023.
Giannis Antetokounmpo shahararran ‘dan wasan kwallon kwando ya lashe lambar yabo ta NBA MVP guda biyu da gasar NBA guda daya. An zabe shi zuwa gasar shahararrun ‘yan wasa kwando karon farko, sau biyar kuma ya buga wasanni bakwai a cikin wasan na fitattun 'yan wasa.
Gwamnatin Najeriya ta bayar da umarnin mayar da hedikwatar hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasa FAAN daga babban birnin tarayyar kasar Abuja zuwa Legas.
Ma’abota sauraron Sashen Hausa na Muryar Amurka na ci gaba da bayyana ra'ayoyin su kan cikar sashen shekaru 45 da fara aiki.
Babban sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Kayode Egbetokun ya kaddamar da wata rundunar musamman da aka yiwa lakabi da “Rundunar Kai Daukin Musamman” da nufin rage yawaitar sace-sacen mutane a babban tarayyar kasar, Abuja.
A yayin ziyarar, sakataren zai yi tsokaci kan yadda Amurka ta kara inganta hadin gwiwar Amurka da Afirka tun bayan taron Shugabannin Amurka da Afirka, da suka hada da yanayi, abinci, da kiwon lafiya.
Gobarar, da ta tashi cikin dare a kasuwar Panteka tsohowa dake cikin garin Kaduna, ta lakume rumfunan masu sayar da katako sama da hamsin kafin zuwan 'yan kwana-kwana wadanda su ka kashe ta.
Mazauna birnin Ibadan, a jihar Oyo da ke kudu maso yammacin Najeriya, mai yawan jama'a sun ji karar fashewar wani abu mai karfi da misalin karfe 7:45 na dare, lamarin da ya haifar da firgici yayin da da dama suka tsere daga gidajensu.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.