Hakan na kunshe ne a cikin rahoton hukumar kididdigar na watan disambar shekarar 2023 dake bin diddigin hauhawar farashin kayayyakin masarufi da aka fitar a jiya litinin.
A wani rahoton da Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta jihar Neja ta fitar a karshen shekara ta 2023 ya nuna cewa da ga shekarar 2017 zuwa wannan lokaci sama da garuruwa 335 ne Mutanensu suka tarwatse a cikin kananan Hukumomi 14 na jihar Nejan saboda Matsalar Hare Haren yanfashin Dajin
Kotun kolin Najeriya ta jingine yanke hukuncin kan karar kujerar gwamnan jihar Nasarawa, zuwa wata rana da zata sanar nan gaba.
Uwargidan shugaban kasar Najeriya Remi Tinubu, ta bi sahun jama'ar da suka yi tir da Allah wadai da kisan wata daliba da aka sace tare da wasu 'yan uwanta mata guda biyar, inda ta bayyana hakan a matsayin "mummunan rashi".
Matatar man fetur mafi girma a nahiyar Afirka ta fara aiki a Najeriya, kamar yadda kamfanin ya bayyana, wanda ya kawo karshen tsawon shekaru da aka kwashe ana jiran soma aikin masana'antar.
A makon da ya gabata ‘yan bindiga sun kwashe mutane da dama a sassan birnin Abuja, sai dai wanda ya fi jan hankali shine lamarin da ya faru a yankin karamar hukumar Bwari da ta hada iyaka da jihohin Kaduna, Nassarwa da Naija.
Daga daya zuwa gomasha biyar ga Jana'irun kowace shekara, gwamnatin Najeriya, kama da ga matakin tarayya har zuwa jihohi, sukan gudanar da bukukuwa na tunawa da sojojin da suka sadaukar da rayukan su wajen ganin kasar ta tsayu da kafafunta.
Wasu ‘yan bindiga da ba’a san su ba sun kashe mutane goma sha uku, ciki harda Jauron Wuro Musa wanda Shine Shugaban masu anguwanni na karamar hukumar Yorro a jihar Taraba.
A ranar Lahadi ne mataimakin shugaban kasar Najeriya Kashim Shettima ya bar Abuja domin halartar taron shekara-shekara na dandalin tattalin arzikin duniya a Davos na kasar Switzerland da za a gudanar daga ranar 15 zuwa 19 ga watan Janairu, 2024.
Sama da kwanaki arba'in da harin jirgin sojan da su ka ce kuskure ne a garin Tudun Biri, wasu al’ummar yankin sun ce har yanzu gwamnati ba ta cika musu alkawurran da ta dauka ba.
Dan wasan Equatorial Guinea Ivan Salvador ne ya fara zura kwallo a ragar Najeriya a minti na 36
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.