Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA) ya cika shekaru 45 da fara watsa shirye-shiryensa.
A ranar 21 ga watan Janairun 1979 aka bude sashen wanda ake saurare a sassa daban-daban na duniya.
Mafi aksarin masu sauraren wannan kafa wacce gwamnatin Amurka ta bude a zamanin mulkin tsohon shugaban Amurka , Jimmy Carter, na zaune ne a Najeriya, Nijar, Ghana, Kamaru da sauran sassan duniya.
Muryar Amurka na da wakilai a Najeriya, Nijar, Ghana, Kamaru da nahiyar turai.
Hedwakatar Sashen Hausa na Muryar Amurkan na Washington D.C., babban birnin Amurka.
Sakonnin Taya Murna
“Inda duk a ke Hausa a Afirka, ba Najeriya kadai ba, kowa na saurarenku.” In ji Tsohon shugaban mulkin soja a Najeriya, Janar Ibrahim Badamasi Babangida.
Dangane da irin shirye-shiryen da VOA Hausa ke watsa wa, Babangida ya ce, “abubuwan da kuke sakawa suna da kyau kwarai da gaske, ina muku fatan alheri, Allah ubangiji ya sa ku ci gaba da fadakar da al’umar duniyar nan baki daya.”
“Sashen Hausa na Muryar Amurka, kafa ce ta duniya wacce mutane ke dogaro da ita a yammcin Afirka don samun bayanai. Wannan kafa ta Muryar Amurka ta taimaka wajen yada harshen Hausa a duniya gaba daya.” In ji tsohon gwamnan Sokoto, Aliyu Magatakarda Wamako.
“Voice of America an santa da ma a ko ina a duniya musamman Hausa Service, tun da Allah har ya taimaka ta kai shekara 45. Sai mu ce muna taya ta murna. Abu ne mai kyau idan aka yi a yaren Igbo da Yarbawa.” In ji Tsohon gwamnan jihar Imo Rochas Okorocha.
“Muna alfahari a matsayinmu na Hausawa, wannan gidan rediyo abin a yaba ne kuma abin a saka musu albarka ne.” Cika Soron Minna, Alhaji Suleiman Yahaya Babangida – Najeriya.
“Ina sauraren Muryar Amurka tun ina dan saurayi. Shirye-shiryen ‘Tsaka Mai Wuya,’ ‘Kasuwa A Kai Miki Dole,’ ‘Noma Tushen Arziki,’ ‘Lafiya Uwar Jiki,’ ‘Nakasa ba Kasawa ba,’ wallahitallahi, wadannan sun sa musamman mata sun fahimci abin da ake nufi kan batun harkar lafiya.” Shugaban kungiyar SIEN ta ‘yan kasuwar Import Export Alhaji Yacouba Dan Maradi daga Nijar.
“Muna muku godiya saboda labaru masu inganci da kuke ba mu, wannan gidan rediyo naku yana da babban aminci. Gidan rediyo ne da kasashenmu na Afirka suke amfani da shi. Muna taya ku murna.” Shugaban kungiyar kare hakkin dan adam ta CODDAE a Nijar, Alhaji Moustapha Kadi.
“VOA na taimakon wanda ke jin Hausa wanda ma ba Bahaushe ba wajen samun labaran duniya, Najeriya, Togo, Ghana inda za ka ji kamar a gabanka aka yi abu.” Babban Lauya a Ghana, Anas Muhammad.
“Ina taya gidan rediyon Muryar Amurka murnar cika shekara 45. Da ka tashi a nan Ghana karfe biyar abin da ya faru a duk duniya baki daya za ka ji shi a Muryar Amurka.” Hajiya Hafsat Kadiri, ‘yar jarida a Ghana
“Shekaru 45 na ilimantarwa, fadakarwa, nishadantarwa, na kuma fahimtarwa. Labarai da babu son kai da labartawa mutane abin da ya kamata su sani. Saboda haka ne muke bin VOA.” Moussa Ousseini, mai magana da yawun babban attajiri a Kamaru, Alhaji Baba Danpullo.
“Wannan tasha ta Muryar Amurka VOA, tasha ce mai taka rawar gani a gaskiya. Kuma muna kaunarta, shi ya sa muke kallonta muke saurarenta, kamar shirin Taskar VOA da Lafiyarmu. Gaskiya tasha ce da ake saurarenta a nan Kamaru.” Abdullahi Sadou, gogaggen dan jarida / shugaban Talabijan Hausa 7
Dandalin Mu Tattauna