Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyar Kwadago Ta Ki Amincewa Da Umarnin Hana Ma'aikata Saka Dogayen Kaya A Neja


Sabon gwamnar Jihar Neja
Sabon gwamnar Jihar Neja

Gwamnan jihar Umar Muhammad Bago, ya bayar da wannan umurni ne a wani jawabi da ya gabatar a lokacin kaddamar da wani aikin noman shinkafa a jihar a ranar Lahadi.

Kungiyar Kwadago ta Najeriya reshen jihar Neja ta nuna rashin amincewa da umarnin gwamnan jihar, Umar Muhammad Bago, na hana ma’aikata saka manyan kaya zuwa aiki daga ranar Litinin zuwa Alhamis.

Gwamnan ya bayar da wannan umurni ne a wani jawabin da ya gabatar a lokacin kaddamar da wani aikin noman Shikafa a jihar a ranar Lahadi.

Kungiyar Kwadago ta ce umarnin da gwamnan ya bayar ba shi da wani tasiri, domin duk wani tsari na aikin Ggwamnati a jihar yana karkashin doka, kamar yadda shugaban kungiyar Kwadagon jihar Neja, Kwamred Abdulkarim Lafane ya fada.

Tuni dai masana kundin tsarin mulkin Najeriya suka fara sharhi kan wannan lamari, Barista Ibrahim Zuru, lauya ne mai zaman kansa a jihar Neja, ya ce babu tsarin tilasta daina sanya doguwar riga a lokacin aikin Gwamnati a jihar Neja, sai dai gwamna ya tilastawa ma’aikatansa.

Hon. Attahiru Musa Abubakar, Ya ce yana ganin akwai bukatar a yi wa maganar da gwamnan ya yi kyakkyawar fahimta a kan wannan lamari.

A yanzu dai kallo ya koma a tsakanin ma’aikatan jihar Neja da kuma gwamnatin jihar domin ganin yadda wannan tirka-tirka za ta kaya.

Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG