Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Farashin Kayan Masarufi Ya Kara Hauhawa A Najeriya


Kayan masarufi a wata kasuwar Abuja a Najeriya
Kayan masarufi a wata kasuwar Abuja a Najeriya

Hukumar Kididdiga Ta Kasa a Najeriya, NBS, ta ce farashin kayayyaki a kasar ya kara hauhawa, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata, kuma rabon da kasar ta ga hakan tun a shekarar 1996.

Kasar dai na fuskantar hauhawar farashin kayan masarufi da sauran nau'ukan kayayyakin amfanin yau-da-kullum babu kakkautawa.

A rahoton da ta fitar, hukumar kididdiga ta kasa NBS, ta ce an samu karin hauhawar farashin kayayyaki a watan Nuwamba da kashi 0.87 cikin 100, idan aka kwatanta da watan Oktoban da ya gabata.

Hauhawar farashin kaya a Najeriya yanzu ya haura kashi 27.33 cikin 100 zuwa kashi 28.20 ciki 100, bisa kididdigar ta NBS, kuma rabon da kasar ta shiga irin wannan yanayi na tashin farashin kayayyaki tun 1996.

Kazalika, hukumar ta ce wannan mataki na hauhawar farashin kaya ya karu da kashi 6.73 cikin 100, idan aka kwatanta da watan Nuwamban shekarar 2022, wanda ya ke a matakin kashi 21.47 cikin 100.

Rahoton, ya ce hauhawar farashin kayayyaki na watan Nuwamba ya wuce adadin da aka kiyasta a watan Oktoba da ya wuce, rahoton ya ce hauhauwar farashin kayan abinci ya karu da kaso 32.84 cikin 100 a shekarar 2023, idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata wanda yake a matakin kaso 24.13 cikin 100.

Rahoton, ya kara da cewa kayayyakin da suka ta'azzara hauhawar farashin sun hada da farashin Burodi, cimaka, man-girki, doya da kuma dankalin turawa, sauran kayakin sune kifi, nama da saura kayakin kwalama da kuma na shayi.

Da yake amsa tambaya ko mene ne ke kawo hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, Dakta Isa Abdullahi Kashere, manazarci kuma masanin tattalin arziki a Jami'ar Tarayya da ke Kashere Jihar Gombe, ya ce "dogaro da kayayyakin da ake shigowa da su daga ketare na taimakawa wajen hauhawar kayayyaki a Najeriya, ganin cewa tashin farashi ya shafi kasashen duniya da dama.

'Yan Najeriya dai na dakon ganin irin dabaru da gwamnatin kasar zata fito da shi domin kawo karshen yadda farashi kayayyaki ya ke tashi a kasar.

Saurari cikakken rahoton Rukaiya Basha:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG