Wanan na zuwa ne bayan da Majalisar ta tabbatar da an ware Naira triliyan 18.324 a matsayin kudin shiga daga jimlar kudin da za a kashe na Naira triliyan 27.503. Amma kuma akwai gibin Naira triliyan 9.18 da dole a cike shi.
A zaman da aka gudanar kan kasafin kudin, a karkashin shugaban kwamitin kudi na Majalisar dattawa, Sanata Mohammed Sani Musa, an tantance shirye - shirye da manufofin wadannan hukumomi da tunanin mai yiwuwa su fuskanci kalubalen kudi a badi, inda aka ba su shawarar su yi kokarin wuce wadannan manufofin domin kasafin kudin na shekara mai zuwa ya ta'allaka ne kan hada rancen kudi daga cikin gida da waje, da kuma kudaden da ake samu daga mayar da hannun jari don cike gibin da ake hasashe.
Da ya ke tsokaci kan batun, Ministan Kula da Kasafin Kudi Wale Edun ya yi amanna da shawarwarin 'yan majalisar, inda ya ce mai yiwu ne, gwamnatin tarayya za ta kawo bukata kara yawan kasafin kudin shekara 2024, amma idan ta samu karin kudaden shiga da ta aiyyana za ta samu.
Saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna