Kungiyar ‘yan tawayen Sudan ta hallaka fiye da mutane 200 a hare-haren kwanaki 3 data kai kudancin Khartoum, a cewar wata kungiyar sa idanu a yau Talata, yayin da gwamnati ke cewar anihin adadin wadanda suka mutun ya ninka hakan.
Ma’aikatar wajen kasar, da ke biyayya ga rundunar sojin a yakin da take gwabzawa da ‘yan tawayen na RSF, “tace an hallaka mutane 433, ciki harda jarirai”.
Harin RSF a kan jihohin Al-Kadaris da Al-Khelwat dake gabar kogin Nilu - masu tazarar kimanin kilomita 90 daga babban birnin kasar - ya tilastawa dubban mutane arcewa daga gidajensu, kamar yadda ganau suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Tun a Asabar din data gabata, mayakan RSF suka shiga zartar da hukuncin kisa da yin garkuwa tare da tilasta bacewar wasu mutane da kuma satar dukiyoyin farar hular da basa dauke da makami, a cewar wata kungiyar lauyoyin wucin gadi, dake tattara bayanan take hakkin dan Adam.
Harin-da lauyoyin suka bayyana da kisan kiyashi - ya haddasa jikkata da bacewar daruruwan mutane, a cewar kungiyar, inda wasu mazauna yankin suka nutse a ruwa sakamakon harbin da aka yi musu yayin da suke kokarin ketare kogin Nilu.
Tun bayan da yaki ya barke a watan Afrilun 2023, ake zargin rundunar sojin kasar da kungiyar ‘yan tawayen da aikata laifuffukan yaki.
An sha zargin kungiyar RSF, wacce a watan da ya gabata Amurka ta zartar da cewa ta aikata kisan kiyashi, da zartar da hukuncin kisa nan take da kisan kare dangi da kuma tsararren cin zarafi ta hanyar lalata.
Yakin ya yi sanadiyar mutuwar dubun dubatar mutane, da tilastawa fiye da mutum miliyan 12 barin gidajensu tare da haifar da abin da kwamitin ceto na kasa da kasa ya kira da matsalar ba da agaji mafi girma da aka taba gani a tarihi.”
Dandalin Mu Tattauna