Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin Yankin Tigray Na Son Sulhu


 Abiy Ahmed
Abiy Ahmed

Wasu manyan jagororin yankin Tigray na kasar Habasha na kiran da a aiwatar da dukkan matakai na yarjejeniyar Pretoria.

Shugabannin yankin Tigray na kasar Habasha sun yi kiran da a yi cikakkiyar aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma a Pretoria (Afurka Ta Kudu) wadda ta kawo karshen tashin hankali tsakanin gwamnatin tarayyar Habasha da ‘yan tawayen Tigray a 2022.

A taron kungiyar Tarayyar Afurka da aka yi a karshen mako a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha, inda kungiyar ta fitar da wani rahoto game da yarjejeniyar, manyan shugabannin Tigray biyu, wadanda su ka kuma kasance abokan gaba a siyasance a baya, sun yi kira ga kungiyar tarayyar Afurka (AU) da ta sa ido kan batun aiwatar da yarjejeniyar

Yarjejeniyar da AU ta taimaka aka cimma, wadda aka kammala a watan Nuwamban 2022, ta tanaji kawo karshen tashin hankali, da mayar da mutanen da aka raba su da muhallansu, da kwance damara, da ci gaba da ayyukan jinkai, da kuma maido da harkokin jama’a kamar yadda suke a baya.

Yarjejeniyar ta yi nasarar kawo karshen tashin hankalin da aka shafe shekaru biyu ana yi tare da maido da wasu daga cikin hidimomin yau da kullum.

Watanni biyu kawai da su ka gabata, aka kaddamar da mataki na farko na aiwatar da yarjejeniyar kwance damara ta Pretoria, wato shirin rushe bangarori da kuma sake hada kan jama’a, wanda aka fi sani da DDR a Tigray. Shirin DDR na da zummar kwance damarar mayaka wajen 371,971 a Habasha, ciki har da mayaka wajen 75,000 daga yankin Tigray.

Jagororin na Tigray su ne Shugaban gwamnatin wuccin gadin Tigray, Getachew Reda, wanda ma a lokacin shi ne ya rattaba hannu a madadin kungiyarsu ta TPLF da kuma shugaban kungiyar ta TPLF na yanzu, Debretsion Gebremichael.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG