Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tarayyar Turai Ta Yi Sammacin Jakadan Rwanda Kan Rikicin Congo


Kwararru a Majalisar Dinkin Duniya sun ce a zahiri Rwanda ce take iko da kungiyar ‘yan tawayen M23 kuma akwai akalla dakarunta 4, 000 da ke yaki tare da su.

A yau Juma’a tarayyar Turai (EU) ta yi sammacin jakadan kasar Rwanda domin neman Kigali ta janye dakarunta daga makwabciyarta jamhuriyar dimokradiyyar Congo tare da dakatar da marawa hare-haren da kungiyar ‘yan tawayen M23 ke ci gaba da kaiwa baya.

Mayakan ‘yan tawayen M23 sun kwace yankuna da dama na yankin gabashin jamhuriyar Congo mai arzikin ma’adinai, ciki har da manyan biranen Goma da Bukavu, sakamakon karancin turjiya daga dakarun sojin kasar.

“A yau tarayyaer Turai ta yi sammacin jakadan kasar Rwanda saboda ci gaba da kai hare-haren da rundunar sojin Rwandan da mayakan M23 ke yi a gabashin jamhuriyar dimokiradiyar Congo (DRC),” kamar yadda EU ta bayyana a cikin wata sanarwa.

“Dole gwamnatin Rwanda ta gaggauta janye dukkanin dakarunta daga yankunnan kasar congo tare da dakatar da goyon bayan da take baiwa M23 da sauran kungiyoyin ‘yan bindiga.”

Kwararru a Majalisar Dinkin Duniya sun ce a zahiri Rwanda ce take iko da kungiyar ‘yan tawayen M23 kuma akwai akalla dakarunta 4, 000 da ke yaki tare da su.

Sai dai Kigali ta musanta hannu a rikicin sannan tace tana fuskantar barazana daga mayakan kabilar Hutu da ke Congon.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG