Safiyar da ta gabata kafin mayakan M23 su isa kewayen Bukavu, birnin mai yawan mutane miliyan 1.3 wanda ke tazarar kilomita 101 kudu da birnin Goma dake hannun ‘yan tawayen, mazauna yankin sun bazama a kan tituna suna yunkurin tserewa kana ‘yan fashi suna cika buhu da duk abin da suka samu.
Da yammacin ranar Asabar, an dan samu kwanciyar hankali a Bukavu lokacin da aka daina harbe-harbe bayan da sojojin Congo suka fice daga birnin kana suka tuka motocinsu zuwa kudu, in ji wani mazaunin Bukavu Alexis Bisimwa.
Mutane da dama sun jira a cikin gidajensu, inda suka kasance cikin fargaba yayin da aka kona gawarwaki aka zuba su kan titi da kuma ‘yan fashi da suka mutu yayin da suka cikin gibin da sojojin Congo suka bari bayan da suka tsere daga inda suke.
Wani mazaunin yankin da ke cikin mutanen da suka tsere suna neman mafaka a ranar Asabar mai suna Alain Iragi, ya ce “Sun cinnawa makamai da harsashansu da suka kasa kwashewa wuta.”
Rahotanni da hotunan bidiyo a shafukan sada zumunta sun nuna an wawashe masana’antu a yankin kana mutane sun gudu daga kurkuku yayin da wutar lantarki ta cigaba da kasancewa kana layukan sadarwa na bude a wasu wurare.
“Wannan abin kunya ne. Wasu ‘yan kasa sun mutu sakamakon harsashai da suka kauce hanya. Ko wasu sojojin ma sun cigaba da kasancewa a cikin birnin kuma suna da hannu a cikin warwason dukiya,” in ji wani dan shekara 25 mazaunin wata anguwa da ‘yan fashi suka afka mata, yana fadawa kamfanin dillancin labaran Associated Press.
Dandalin Mu Tattauna