Daruruwan masu zanga-zangar ne suka rike da allunan da aka rubuta “Na gode wa Shugaba Trump” tare da nuna wasu sakonni na sukar abin da suke kallo a matsayin dokokin wariyar launin fata da gwamnatin Afirka ta Kudu ta kafa da ke nuna wariya ga 'yan tsiraru.
Da yawa sun fito ne daga al'ummar Afrikana da Trump ya mayar da hankali a kai a cikin wani umarni na zartarwa mako guda da ya gabata, wanda ya yanke taimako da tallafi ga gwamnatin Afirka ta Kudu karkashin jagorancin bakar fata. A cikin wannan tsari, Trump ya ce ‘yan Afrikan na Afirka ta Kudu, wadanda galibinsu ‘ya’yan Turawan mulkin mallaka ne na Holland, suna fuskantar wata sabuwar doka da ta bai wa gwamnati damar kwace filayen mutane masu zaman kansu.
Gwamnatin Afirka ta Kudu ta musanta cewa sabuwar dokar ta na da alaka da kabilanci, kuma ta ce ikirarin da Trump ya yi kan kasar da kuma dokar na cike da munanan bayanai da kuma gurbatattun bayanai.
Trump ya ce ana kwace filaye daga yan Afrikana - wanda umarnin ya kira “kwacewa gonaki saboda kabilanci” - yayin da ba a kwacewa kowa gona ba karkashin wannan doka ba. Trump ya kuma sanar da wani shiri na bai wa ‘yan Afrikana matsayin ‘yan gudun hijira a Amurka Su bangare daya ne kawai na tsirarun farar fata na Afirka ta Kudu.
Dandalin Mu Tattauna