Daga cikin shawarwarin da suka tsayar, mahalarta taron sun bukaci sojoji su gudanar da mulkin rikon kwarya na shekaru 5, wa’adin da a kan iya sake sabuntawa idan bukatar hakan ta taso, yayin da Janar Tiani zai yi rantsuwa a nan gaba a matsayin shugaban kasa mai cikakken iko.
Shugaban gwamnatin mulkin sojan ta Nijar ya ce wa mahalarta taron sun yi aikinsu, shi ma zai yi nasa ba tare da wata jikara ba.
Sanarwar karshen taron ta jaddada Nijar a matsayin cikakkiyar jamhuriya saboda haka mahalartan sun zo da shawarar amfani da wani kundin tsarin mulki da aka kira Charte de la Refondation.
Sannan taron ya bukaci Janar Abdourahamne Tiani ya ja ragamar ta tsawon shekaru 5 daga ranar da aka saka hannu kan wannan kundi a matsayin shugaban kasa mai cikakken iko, akwai yiwuwar sabunta wannan wa’adi idan ta kama ta la’akari da tabarbarewar sha’anin tsaro.
Haka kuma mambobin CNSP na da damar shiga zabubuka idan suna da ra’ayi sannan an zo da shawarar kara wa Janar Tiani igiya daga Brigadier General zuwa Janar mai Tauraro 5 General d’armee.
An kuma zo da shawarar rushe dukkan jam’iyun siyasa tare da takaita yawansu a nan gaba.
Yaki da cin hanci da farautar wadanda suka handami dukiyar kasa a zamanin mulkin farar hula da hukunta wadanda ake zargi da hannu a mutuwar tarin sojoji a yayin hare-haren ta’addancin da aka fuskanta a Inates Chinagoder da dai sauransu.
A jawabinsa shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar ya jinjinawa tawagogin da suka fito daga illahirin jihohiin kasa domin halartar wannan zama. Ya na mai cewa an yi aiki cikin natsuwa.
Yace har yanzu kofofi na bude domin tattara shawarwarin ‘yan kasa saboda haka kenan ya bukaci daukacin ‘yan Nijar su ci gaba da aika wa da gudunmawar shawarwarin da suke ganin zasu taimaka a sami mafita.
Kimanin wakilan 716 da aka karkasa a kwamitoci 5 ne suka gudanar da nazari kan matsalolin da ake hasashen sune suka dabaibaye kasa a tsawon gomman shekaru na mulkin farar hula.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna