A jiya Juma’a Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya tabbatar da wani daftari na bai daya da ya bukaci kungiyar ‘yan tawayen M23 a Gabashin Dimokaradiyar Jamhuriyar Congo ta gaggauta kawo karshen zub da jini kana ta janye daga yankunan da ta kwace. Kwamitin ya kuma yi barazanar aza takunkumi a kan wadanda suka tsawaita yakin.
Faransa da ta shirya daftarin, ta aike da wani bayyanannen sako cewa babu wani matakin sasantawa na soja da za a dauka a rikicin na gabashin DR Congo.
"Manufa itace cimma yarjejeniya mai inganci, ba tare da sharadi ba kuma cikin gaggawa." In ji Jakada Nicolas de Riviere. Ya ce “Ana bukatar maido da tattaunawa cikin gaggawa, tare da taimakon shiga tsakani a mataki na yanki. Wajibi ne a mutunta ‘yancin da kuma tsare yankunan Dimokaradiyar Jamhuriyar Congo."
Daftarin ya kuma yi kira ga sojojin Rwanda da su daina taimakawa kungiyar M23 kana su gaggauta janyewa daga DR Congo ba tare da gindaya wasu sharuda ba. Mambobin kwamitin sun zargi sojojin Rwanda da bada taimako kai tsaye ga kungiyar M23. Rwanda dai ta sha musunta wadannan zargi-zargin cewa tana taimakawa ‘yan tawayen.
Kwamitin Sulhun MDD ya yi kira da kakkausar murya ga DR Congo da Rwanda da su koma ga tattaunawar diflomasiya cikin gaggawa ba tare da gindaya wani sharadi ba kana su aiwatar da yarjejeniyoyin yankin na Luanda da kuma Nairobi da aka cimmawa a baya.
Dubban ‘yan tawayen M23 masu samun goyon Rwanda suna ci gaba da kwace yankunan gabashin DR Congo mai arzikin albarkatun karkashin kasa ba tare da samun wani turjiya daga sojojin gwamnati ba.
Tun cikin tsakiyar watan Disamba, sun maida hankali a kan larduna a Arewa da Kudancin Kivu masu arzikin albarkatun karkashin kasa, inda suka kwace Goma babban birinin Kivu ta Arewa a karshen wata janairu kana suka shiga Bukavu babban yankin Kivu ta Kudu a ranar 14 ga watan Faburairu.
Dandalin Mu Tattauna