Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Congo: Dannawar ‘Yan Tawaye Zuwa Garin Uvira Ya Haddasa Fargaba


Tun bayan kwace iko da garin Bukavu, dakarun sojin Congo da ke janyewa suka kare da gwabza fada da kungiyar ‘yan bindigar da ke kawance dasu da ake kira da Wazelendo wacce ke adawa da janyewar.

A yau Laraba, an jiyo karar manyan bindigogi a garin Uvira dake kan iyakar gabashin jamhuriyar Dimokiradiyar Congo, a cewar majiyoyin yankin, inda fada ya barke tsakanin dakarun dake kwance da bangarorin 2 a yayin da ‘yan tawayen M23 masu samun gogyon bayan kasar Rwanda ke kara dannawa zuwa yankin.

Al’umma da jami’an yankin sun bada rahoton yadda ake ta sace-sace da warwatse gawawwaki a kan tituna da kuma yadda sojojin gwamnatin Congo ke arcewa daga yankin ta tafkin Tanganyika cikin kananan jiragen ruwan zamani. inda suka ce, kurkukun dake yankin ya zama babu kowa a cikinsa.

‘Yan tawayen M23 na cigaba da nausawa kudanci zuwa garin Uvira, wanda keda iyaka da kasar burundi ta hanyar wani tafki, tun bayan da suka kwace iko da babban birnin lardin, Bukavu, a karshen makon daya wuce-asara mafi girma da Congo tayi tun bayan da aka kwace iko da birni mafi girma a yankin, Goma, a karshen watan Janairun daya gabata.

Rahotannin shigar ‘yan bindiga cikin garin Kamanyola a jiya Talata ya haddasa fargaba a Uvira, mai tazarar kilomita 80 daga kudu.

Tun bayan kwace iko da garin Bukavu, dakarun sojin Congo da ke janyewa suka kare da gwabza fada da kungiyar ‘yan bindigar da ke kawance dasu da ake kira da Wazelendo wacce ke adawa da janyewar.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG