Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mahalarta Babban Taron Nijar Sun Ba Da Sharuddan Da Suke Son A Shigar Cikin Kundin Tsarin Mulkin Kasar


Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani
Shugaban gwamnatin mulkin sojan Nijar Janar Abdourahamane Tiani

Mahalarta babban taron kasa a Nijar na ci gaba da tafka muhawara tare da bullo da shawarwarin da suke fatan ganin an shigar da su a kundin tsarin mulkin rikon kwaryar kasar a ci gaba da yunkurin mayar da ita kan tafarkin dimokradiyya

Batun wa’adin gwamnatin rikon kwarya da adadin jam’iyyun siyasa da na bukatar shimfida shari’ar Musulunci na daga cikin shawarwarin da wasu mahalartan suka gabatar, sai dai kawo yanzu ba a cimma matsaya kan wadannan batutuwa ba.

A wannan Talata da ke matsayin wuni na 4 na babban taron kasa, kwamitoci daban-daban na ci gaba da gudanar da ayyuka babu kama hannun yaro.

A kwamitin da aka dorawa alhakin tattauna sha’anin tattalin arziki mambobinsa sun ce sun gano abubuwan da ke hana ruwa gudu saboda haka suka zo da shawarwarin da ka iya zama mafita a cewar Dr. Soly Abdoulaye.

A nasa bangare kwamitin da ke kula da ayyukan kafa gimshikan Nijar sabuwa ya maida hankali kan ka’idodi da dokokin da za a tafiyar da lamuran mulkin rikon kwarya a karkashinsu. Misali wa’adin gwamnatin rikon kwarya, dokar jam’iyun siyasa da dai sauransu.

Wata shawarar ta daban daga cikin mafi daukan hankula a wannan taro ita ce wacce ta shafi sha’anin doka da shari’ar kasa inda wasu ke ganin bukatar sauya tsarin da aka gada daga turawan mulkin mallaka.

Elhakib Mohamed dake halartan taron a karakshin inuwar gamayyar kungiyoyin Synergie des OSC na daga cikin masu irin wannan ra’ayi.

A gobe Laraba 19 ga watan Fabrairu ake sa ran rufe wannan taro kamar yadda aka ayyana a can farko, koda yake wasu na ganin lokacin ba zai ba da damar tattauna dukkan muhimman matsalolin da suka addabi kasar ba ballantana a iya gabatar da shawarwarin da suka shafi kowanne daga cikin batutuwan da suka fi cinyewa al’umma tuwo a kwarya.

Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:

Mahalarta Babban Taron Nijar Sun Bada Wasu Matakan Shigarwa Kundin Tsarin Mulkin Rikon Kwaryar Kasar.MP3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG