Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ukraine: Putin Ya Shaida Wa Trump Cewa Akwai Yiyuwar Tattaunar Sulhu


Putin / Trump
Putin / Trump

Fadar Kremlin ta bayyana cewa an shafe sa’a daya da rabi ana hira ta wayar tarho kuma Putin da Trump sun amince cewa lokaci ya yi da za su yi aiki tare

Shugaba Donald Trump na Amurka ya bayyana cewa sun yi tattaunawar wayar tarho mai tsawo kuma mai cike da alfanu tsakaninsa da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a jiya Laraba, inda suka amince da fara tattaunawar sulhu domin kawo karshen yakin Ukraine nan take.

Trump ya wallafa a shafinsa na sada zumunta na “Truth Social” cewa dukkanin shugabannin 2 sun mikawa juna goron gayyata domin “kai ziyara kasashen juna,” yayin da shugaban Amurkan yace zai kira takwaransa na Ukraine Volodymyr Zelensky “nan take” domin sanar da shi game da wayar da suka yi da Putin.

A wani yanayi na kyautatuwar alaka na musamman tsakanin Washington da Moscow, a kebe, fadar Kremlin ta bayyana cewa an shafe sa’a daya da rabi ana hira ta wayar tarho kuma Putin da Trump sun amince cewa lokaci ya yi da za su yi aiki tare.”

Putin ya kuma shaidawa Trump cewa akwai yiyuwar sulhunta rikicin Ukraine din da mamayar da Rasha ta yiwa makwabciyarta mai goyon bayan kasashen yamma ya sabbaba a 2022, sannan ya gayyaci shugaban Amurkan zuwa birnin Moscow, a cewar fadar Kremlin.

Wayar Trump da Putin na zuwa ne bayan wata musayar fursunoni da ta faru a makon da muke ciki inda Moscow ta saki wani malamin makaranta ba-amurke Marc Fogel yayin da Washington ta saki wani kwararre a kan harkar kudin kirifto dan asalin Rasha Alexander Vinnik.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG