Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, ya yi gargadi cewa yarjejeniyar tsagaita wutar da Isira’ila ta cimma da Hamas za ta kawo karshe, kuma za a koma yaki gadan gadan har idan dai ba a saki karin mutanen da kungiyar mayakan na Hamas ke rike da su zuwa ranar Asabar ba.
"Rundunar soji za ta koma yaki mai tsanani, har sai an yi galaba kan Hamas," in ji Netanyahu a wani faifan bidiyo jiya Talata.
Tun da farko, Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bada shawara a soke yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin Isra’ila da Hamas, idan Hamas bata saki dukkanin mutanen da take tsare da su ba zuwa ranar Asabar.
Trump ya furta wadannan kalaman ne ranar Litinin, bayan da Hamas ta zargi Isra’ila da saba sharuddan yarjejeniyar tsagaita wutar, kuma ta yi barazanar jinkirta sakin mutane uku, wadanda aka tsai da cewa za a sake su ranar Asabar.
Dandalin Mu Tattauna