A yau Laraba, kungiyar gwamgwarmayar Falasdinawa ta Hamas ta yabawa kasashen Jordan da Masar a kan kin amincewa da raba Falasdinawa da zirin Gaza, abinda Shugaban Amurka Donald Trump ke shirin yi.
Hamas ta jinjinawa matsayar ‘yan uwanmu na Jordan da Masar a kan kin amincewa da sauyawa al’ummarmu matsuguni tare da jaddada cewa akwai shirin kasashen larabawa na sake gina Gaza ba tare da matsar da al’ummarta ba,” kamar yadda kungiyar mai ra’ayin Msulunci ta bayyana.
Kasashen Jordan da Masar, wuraren da Trump ya bada shawarar mayar da al’ummar Gaza fiye da miliyan 2, sun bayyana adawarsu da shirin, wanda ya kunshi karbe iko da yankin Falasdinawan da yaki ya daidaita, a jiya Talata.
A sakon da ya wallafa a shafinsa na sada zumunta, Sarki Abduallah na Jordan, ya jaddada matsayar kasarsa ta yin adawa da sauyawa Falasdinawa matsuguni”, inda ya kara da cewa wannan shine “matsayar kasashen Larabawa bai daya”.
Kalaman shugaban na jordan sun biyo bayan ganawarsa da trump a birnin washington a talatar data gabata.
Dandalin Mu Tattauna