A yau Alhamis kasashen Turan da aka bari cikin duhu sun yi gargadin cewa kazamar yarjejeniyar da Shugaban Amurka Donald Trump ke neman kullawa da Moscow a kan kawo karshen yakin Ukraine ba za ta yi nasara ba-inda suka jaddada cewa dole ne su da Kyiv su samu mazauni a tattaunawar sulhun.
Da ya ke ganawa da kawayensu na rundunar tsaro ta NATO kwana guda bayan da Trump ya bayyana cewa ya amince da fara tattaunawar sulhu da Shugaba Vladimir Putin na Rasha, shugaban ma’aikatar tsaro ta Pentagon Pete Hegseth ya musanta cewa hakan na nufin cin amanar gwagwarmayar yakin da Ukraine ta shafe shekaru 3 tana gwabzawa.
Sai dai matakin na Trump ya baiwa kawayensa na Turai mamaki-inda da dama daga cikinsu suka fito fili suna tuhumar hikimar hakan.
Shugaban Jamus Olaf Scholz ya yi fatali da kowane irin “tsararren sulhu” sannan ministan tsaronsa yace “abin takaici” ne yadda tuni Washington ta fara amincewa da muradan fadar Kremlin.
A wani kakkausan jawabi da ta gabatarwa manema labarai yayin taron NATO a birnin Brussels, babbar jakadiyar tarayyar Turai Kaja Kallas ta nanata cewa babu yarjejeniyar da za’a kulla a bayan idanunsu da za ta yi aiki, sannan ta zargi Washington da kokarin dadawa Rasha.
“Bai kamata mu tsame wani batu gabanin fara tattaunawar ba saboda hakan fadawa tarkon da Rasha ta kafa ne kuma shi ne abin da suke so,” a cewarta.
“Duk yarjejeniyar da aka kulla cikin gaggawa kazama ce,” a cewarta. “Babu yadda za’a yi ta yi aiki.”
Dandalin Mu Tattauna