A yau Talata, Mataimakin Shugaban Amurka JD Vance ya yi gargadi a kan yawan dokokin da ake laftawa kirkirarriyar basira a wani taron koli a kan fasaha da ke gudana a birnin Paris, inda ya ja kunnen kawayensu kasashen Turai da abokan hamayyarsu irinsu China game da tsaurara rikon gwamnatoci.
“Yawan dokoki a kan kirkirarriyar basira na iya kashe bangaren a daidai lokacin da ya ke kokarin fara tashi,” kamar yadda Vance ya shaidawa shugabannin kasashen duniya da na manyan kamfanonin fasaha a birnin Paris.
Ya ware sunan dokar tarayyar Turai a kan fasahar sadarwar zamani domin yin suka “a kan yawan dokokin da ta kirkira a kan sauke wani abu da mutum ya wallafa a dandalin sada zumunta da sanya idanu a kan labaran karya” wadanda yace suna dorawa manyan kamfanonin fasahar Amurka nauyi babu gaira babu dalili.
Vance ya kuma caccaki China a matsayin daya daga cikin “gwamnatocin kama karya” da dama ke nazarin yin amfani da kirkirarriyar fasaha wajen sarrafa al’ummarta a cikin gida da kuma wasu kasashen ketare.
“Hada gwiwa dasu na nufin daure kasarka a karkashin ubangida dan kama karya da ke neman ya kutsa, ya bankado tare da kwace maka hanyoyin samun bayanai,” a cewar Vance.
Ya ba da misali da “fasaha mai araha da aka tulawa tallafi da gwamnatocin kama karya ke fitarwa”, inda yake tsokaci a kan kyamarorin tsaro da na’urorin sadarwar intanet masu karfin 5G da kasar China ke sayarwa a kasashen ketare.
Dandalin Mu Tattauna