Wani harin sojin sama da aka nufi kaiwa ‘yan bindiga ya yi kuskure tare da hallaka wasu mutane 6 a kauyen Yauni dake mazabar Zakka ta karamar hukumar Safanan jihar Katsina.
Mummunan al’amarin, ya jefa al’ummar kauyen cikin kaduwa da rudani.
Galibin wadanda al’amarin ya rutsa dasu daidaikun dangi ne, da suka hada da yara 3, da namiji babba guda da kuma mata 2.
Al’amarin, wanda ya faru bayan kammala zabubbukan kananan hukumomi a asabar din data gabata, ya faru ne sakamakon yunkurin jami’an tsaro na dakile wani harin da ‘yan bindiga suka kitsa kaiwa kan masu kada kuri’a a kauyen Zakka.
Wasu ganau sun ba da rahoton cewar jami’an tsaro, da suka hada da ‘yan sanda da askarawan tsaron jihar (CWC) sun yi zazzafar musayar wuta tsakaninsu da ‘yan bindigar inda aka hallaka jami’an ‘yan sanda 2 da jami’in CWC guda a musayar wutar.
Majiyar ta kara da cewa wani jami’in tsaron, wanda ya samu raunuka da dama, ya mutu daga bisani.
Sai dai, har sa’ilin hada wannan rahoto hukumomin soji dana gwamnati basu ce komai akan faruwar lamarin ba.
Dandalin Mu Tattauna