Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya isa birnin Addis Ababa, na kasar Habasha, don halartar taron kolin shugabannin gwamnatocin kungiyar hada kan kasashen nahiyar Afirka (AU)
Shugaba Tinubu zai gabatar da jawabi yayin taron kwamitin zaman lafiya da tsaro na kungiyar ta AU, inda tattaunawar za ta maida hankali a kan matsalolin tsaron da ke addabar nahiyar a halin yanzu, ciki har da kazancewar rikici a jamhuriyar dimokiradiyar Kongo.
Shugaban wanda ya sauka a Habasha a daren jiya Alhamis, ya samu tarba a filin saukar jiragen sama daga mukaddashin jami’in kula da tsare-tsaren diflomasiya na kasar, Eshetu Legesse da ministan harkokin wajen Najeriya, Jakada Yusuf Tuggar da babban jami’i a ofishin jakadancin Najeriya da ke Habasha, Jakada Nasir Aminu.
An tsara cewa Shugaba Tinubu zai dawo gida Najeriya a ranar Litinin, 17 ga watan Fabrairun da muke ciki.
Dandalin Mu Tattauna