Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Shirin Shiga Kakar Zaben 2027 A Najeriya


Hedkwatar APC
Hedkwatar APC

Gwamnan Kaduna seneta Uba Sani ya ce “al’umma za su sake zaban APC a duk matakai daga sama har kasa. A can sama shine jagoran mu, shugaba Bola Ahmad Tinubu zai yi tazarce a zaben 2027. A matakin jiha kuma, jam’iyyar zata yi nasara, har da matakan majlisar tarayya da ta jihohi da izinin Allah.”

Yayin da Najeriya ta doshi wata kakar zabe, ‘yan siyasa sun fara kintsawa don tunkarar zaben kasar inda manyan ‘yan adawa suke nuna alamun daukan matakan shirin zaben da za ayi a 2027.

Tsohon shugaban Najeriya kuma shugaban mulkin farar hula na farko bayan da kasar ta koma tafarkin demokradiyya bayan mulkin soji Olushegun Obasanjo ya yi wata ganawa da mataimakin shi kuma dan takarar jam’iyyar PDP a zaben 2023 alhaji Atiku Abubakar wanda ya yi tattaki har inda Obasanjon yake.

Manyan ‘yan siyasar sun gana cikin sirri tare da wasu manyanyan ‘yan siyasa.

Sai dai duk da cewa Olushegun Obasanjo bai bada bayana goyon bayan shi ga wani dan takara mai sha’awar tsayawa takara ba, tsoma bakin shi a shirye shiryen da ‘yan adawa suke yi zai iya tasiri sosai ga zaben da ke karatowa.

Ganawar ta su ta biyo bayan wani jawabin da Atiku ya yi a wani babban taro da aka yi a Abuja, inda ya yi kira da neman hadin kan ‘yan adawa su kulla wata hadaka.

Wasu majiyoyi sun sheda cewa Obasanjo wanda ake mashi kallon wani mai fada a ji a fagen siyasar Najeriya, ya zuba ido ya saurari rahoton da tawagar ‘yan adawar suka gabatar.

Wani makusancin tsohon shugaban ya ce “Obasanjo ya fada karara cewa, ziyarar da Atiku ya kawo mai bata da wata alaka da batun burin shi na sake tsaya takara, manufar ziyar shi itace ya yi min bayani a game da shirin hadakar da suke yi don ciyar da Najeriya gaba.”

A wani bangaren kuma, gwamnan Kaduna sanata Uba Sani ya ce “al’umma za su sake zaban APC a duk matakai daga sama har kasa. A can sama shine jagoran mu, shugaba Bola Ahmad Tinubu zai yi tazarce a zaben 2027.A matakin jiha kuma, jam’iyyar zata yi nasara, har da matakan majlisar tarayya da ta jihohi da izinin Allah.”

Sannan a game da batun matsayin ‘yan jam’iyyar kuwa, Uba Sani ya ce “Da wanda ya shiga APC yau da wanda ya dade a jam’iyyar har tsawon shekaru 10, duk matsayin su daya yake. Duk za su more ‘yancin su da duk wata damar da dan jam’iyyar zai more.

Ya kuma kara da cewa, kofofin jam’iyyar APC a bude take ta karbi sabbin tuba, gabanin babban zaben da ke tafe.

Shugabancin jam’iyyar na gari shine silar samun karbuwar da jam’iyyar take yi a matakin tarayya da jihohi, inda ya kara da cewa, jam’iyyar ta samun wurin zama a jihar Kaduna, arewacin Najeriya da ma Najeriyar baki daya.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG