Gwamnatin Najeriya ta sanarda aniyarta ta daukar ma’aikatan lafiya 28, 000 da hukumar raye kasashe ta Amurka (USAID) ke biya albashi, wacce shugaban Amurka Donald Trump ya dakatar da ayyukanta.
A hirarsa da wani shirin tashar talabijin ta Channels mai suna Hard Copy” na Juma’ar da ta gabata, ministan lafiyar Najeriya, Muhammad Ali Pate, ya bayyana cewar gwamnatin na tsare-tsaren zuke ma’aikatan lafiyan zuwa cikin tsarin kiwon kasar tare da rage dogaro akan tallafi daga kasashen ketare.
Ali Pate ya yabawa mahimmanci gudunmowar da gwamnatin amurka ke baiwa najeriya a fannin kiwon lafiya, musamman ma wajen yaki da cutar kanjamau da tarin fuka da kuma zazzabin cizon sauro.
Sai dai, ya jaddada aniyar Najeriyar na karbe iko da fannin lafiyarta tare da rage dogaro da tallafi daga ketare.
Dandalin Mu Tattauna