Hukumomin Amurka sun zayyana sunayen ‘yan Najeriya 201 da za su taso keyarsu zuwa gida a ci gaba da yakin da Shugaba Donald Trump yake yi da bakin haure.
Bakin hauren da za a taso keyar tasu zuwa Najeriyar sun hada da fursunonin da aka yankewa hukunci da sauran wadanda suka aikata nau’ukan laifuffuka daban-daban.
Karamar ministan wajen Najeriya Bianca Odumegwu-Ojukwu ce ta bayyana hakan lokacin da jakadan Amurka a Najeriya Richard Mills ya ziyarceta a gidan Tafawa Balewa, da ke Abuja.
“A halin da ake ciki yanzu, an shaida mana cewar kimanin ‘yan Najeriya 201 na sansanin bakin haure na Amurka, kuma an riga an tantance kimanin 85 domin taso keyarsu zuwa gida. Shin ta wacce hanya zamu sassauta radadin da suke ji?” a cewar Bianca, inda ta bukaci a dawo dasu cikin mutunci kamar yadda mataimakinta na musamman akan harkokin yada labarai da kafafen sada zumunta, Magnus Eze, ya ruwaito a cikin wata sanarwa.
Kalaman na zuwa a daidai lokacin da aka dakatar da tsarin sabunta neman iznin shiga Amurka (biza) ba tare da halartar ganawa ta zahiri ba, abinda zai sanya neman bizar ya kara wahala.
Bugu da kari, ministar ta yi kokarin fayyace rashin tabbas din da ke kewaye da makomar ayyukan hukumar raye kasashe ta Amurka (USAID) a Najeriya, inda ta nemi samun tabbaci ko hukumar zata ci gaba da ayyukanta duk da sauye-sauyen da za’a yi mata anan gaba.
A nasa jawabin, Jakada Mills ya ba da tabbacin cewar gwamnatin Amurka za ta bayyana matsayarta a nan gaba, musamman dangane da tsarin neman biza ta na’ura da kuma makomar hukumar USAID.
Dandalin Mu Tattauna