Gwamnonin shiyar kudu maso yammacin Najeriya sun amince da kafa tsaron hadin gwiwa da nufin dakile matsalar rashin tsaro a yankin.
Hakan na cikin shawarwarin da kungiyar gwamnonin kudu maso yammacin Najeriya ta cimma a taron da ta gudanar a Legas a jiya Alhamis.
“Sakamakon karuwar barazanar tsaro, mun yanke shawarar kafa rundunar tsaron hadin gwiwa domin inganta matakan tsaro a fadin yankin kudu maso yamma,” kamar yadda gwamnan jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya wallafa a shafinsa na X bayan kammala taron na yini daya.
Gwamnan na jihar Legas wanda shi ne shugaban kungiyar ya nanata aniyar gwamnonin ta daukar kwararan matakai domin tabbatar da zaman lafiya da daidaito a tsakanin al’ummominsu”.
Dandalin Mu Tattauna