Mai Shari’a Inyang Ekwo na babbar kotun tarayya da ke Abuja ya amince da bukatar tsohuwar ministar albarkatun man fetur, Diezani Alison-Madueke, ta yin gyara a karar da ke kalubalantar umarnin da hukumar EFCC, mai yaki da masu yiwa tattalin arzikin Najeriya zagon kasa ta samu na kwace kadarorinta a mataki na karshe.
Mai Shari’a Ekwo ya amince da bukatar ne bayan da lauyan Diezani, Godwin Inyinbor, ya gabatar da ita kuma lauyan FCC, Divine Oguru, bai kalubalanci hakan ba.
A yayin zaman na yau, Inyinbor ya shaidawa kotun cewar sun riga sun shigar da bukatar yin gyara a kararsu ta asali kuma sun gabatarwa bangaren wadanda ake kara da kofinta.
Oguru bai kalubalanci bukatar tsohuwar ministar ta yin gyara a karar ba kuma Mai Shari’a Ekwo ya amince da hakan.
Alkalin ya baiwa Diezani kwanaki 5 ta gabatar da gyararriyar kara sannan ya baiwa EFCC kwanaki 14 daga ranar da aka mika mata kofen gyararariyar karar ta mayar da martani.
Daga bisani an dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan Maris mai kamawa domin ci gaba da shari’a.
Dandalin Mu Tattauna