Wani jami’i ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar, a yau Talata kasar Libya ta mayar da bakin haure 369 zuwa kasashensu na asali; Najeriya da Mali ciki harda mata da yara kanana fiye da 100
Shugaban Hukumar kula da Gidajen Yarin Najeriya, Hailey Nababa ne yayi wannan gargadi a sanarwar daya fitar yau Talata a Abuja.
Kamfanin ya wallafa a shafinsa na X cewa, “Muna sanar wa abokan hulda cewa zamu rufe ofisoshinmu dake fadin Najeriya a yau, 30 ga watan Yulin 2024.”
A cewar Muhammad Idris, matakin na cikin jerin matakan da gwamnatin Shugaba Tinubun ke dauka na saukaka rayuwar ‘yan Najeriya.
Binciken da rundunar ‘yan sandan kasa da kasa (INTERPOL) ta gudanar ya nuna cewa duk bayan sa’a guda, ana fitar da dubban daruruwan dalolin haramun daga Najeriya zuwa sauran sassan duniya.
A yayin aikin hajji na bana dai, hukumar NAHCON ta kayyade kudin da maniyatta za su biya a kan dala dubu 5 da 692.25 a madadin wanda aka tsara a farko-farko na dala dubu 6 da 401.31 inda aka sami ragin dala 700 da centi 6 a bisa ana canjin naira zuwa dala a kan naira 456 a waccan lokaci.
A wata hira ta wayar tarho da gidan talabijin ta Channels, Shugaban karamar hukumar Konduga, Abbas Ali Abari, ya tabbatar da afkuwar lamarin sai dai ya ce bashi da adadin wadanda al’amarin ya rutsa dasu.
Masu zanga zangar nuna takaici game da matsalar yunwa da tsadar rayuwa a Najeriya sun fara daukar matakin datse babban titin Abuja zuwa Kaduna da sanyin safiyar ranar Litinin 29 ga watan Yuli.
Tinubu ya sanya hannu a dokar a Fadar gwamnati da ke Abuja a ranar Litinin a lokacin taron majalisar zartawa da aka saba yi a kowane mako.
An samu dogayen layukan man fetur a wasu manyan biranen Najeriya a ranar Litinin bayan da kamfanin mai na NNPC ya fuskanci matsalar samar da mai ga ‘yan kasuwa da gidajen man fetur na cikin gida.
Amurka da Birtaniya da kuma Canada sun fitar da sanarwar gargadi ga ‘yan kasashensu mazauna a Najeriya, kan su zauna cikin shiri kan yiwuwar barkewar rikici yayin zanga-zangar da aka shirya za a yi a kasar.
Domin Kari
No media source currently available