Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Fitar Da Daruruwan Haramtattun Daloli Daga Najeriya Duk Sa'a Guda - Interpol


INTERPOL, Lyon
INTERPOL, Lyon

Binciken da rundunar ‘yan sandan kasa da kasa (INTERPOL) ta gudanar ya nuna cewa duk bayan sa’a guda, ana fitar da dubban daruruwan dalolin haramun daga Najeriya zuwa sauran sassan duniya.

Mataimakin shugaban Interpol na nahiyar Afirka, Garba Umar, ne ya bayyana haka a Abuja a jiya Litinin yayin da yake kaddamar da taron bada horo ga jami’an tsaro na yini 4 a kwalejin horaswa ta hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC), dake Abuja.

Hedkwatar Hukumar EFCC Da Ke Abuja
Hedkwatar Hukumar EFCC Da Ke Abuja

A cewar Umar, matsalar halasta kudaden haram a nahiyar afrika dama duniya baki daya ta kai wani mummunan mataki amma rundunar interpol ta tsara matakan shawo kan matsalar.

“Akwai hujjojin dake nuna cewar duk bayan sa’a guda, dubban daruruwan daloli na zurarewa daga Najeriya zuwa wasu sassan duniya, inda ake halastasu kafin su fada aljihun batagari domin su more ladan laifuffukan da suke aikatawa, a yayin da illar yin hakan kai karewa a kan mutanen kirki masu neman na kansu.”

Wasu haramtattun kudade a Hong Kong
Wasu haramtattun kudade a Hong Kong

Ya kuma jaddada cewa masu halasta kudaden haramun na shirin shiga tasku kasancewar tsauraran matakan da Interpol ke dauka zasu takaita irin wannan fataucin a fadin duniya.

Da yake sharhi akan taken taron bada horon: “bada horo da tabbatar da hadin kai a yakin da ake yi da laifuffukan da suka shafi kudi”, Umar ya kara da cewa laifuffukan da suka shafi kudi sun zama wani al’amari tsakanin kasa da kasa don haka akwai bukatar baiwa jami’an tsaro horo akai-akai domin su zarta tunanin ‘yan damfara.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG