Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto, ASP Ahmad Rufa’i, ya tabbatar wa da Muryar Amurka cewa, ‘yan bindiga sun sace Sarkin Gobir tare da dan sa.
Masana tattalin arziki a Najeriya na ci gaba da yin fashin baki kan tasirin takaddamar da ke wakana tsakanin kamfanin tace man Dangote da hukumar kula da cinikayyar mai ta Najeriya. Matatar man ta Dangote ta ce a watan Agusta za ta fara fitar da fetur din da ta tace a kasuwannin kasar.
Rahotannin sun bayyana cewa mabiya Dauda Kahutu Rarara a shafin sada zumunta na Facebook da yawa sun tura sakonnin neman a cire shafin mawakin daga dandalin, saboda wata wakar yabo da ya yi wa gwamnatin Najeriya kwanan nan.
Sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh, ta fitar a yau Juma’a tace, rundunar ta tura jami’anta dubu 4 da 200 domin shawo kan duk wani nau’in tashin hankalin da ka iya tasowa yayin zanga-zangar.
Wani mazaunin garin Buni Yadin, Ali Hassan ya shaidawa tashar talabijin ta Channels ta wayar tarho cewar, al’amarin ya faru ne da misalin karfe 12 da rabi na ranar yau Juma’a, kuma ya raunata wata yarinya.
“A yadda ‘yan bindiga suke ta addabar jama’a a Zamfara, Sokoto da Katsina, me ya sa hukumomin tsaro ba su iya gano masu yin wadannan ayukan ba, sai yanzu da mutane suka fito za su yi zanga-zanga akan wahalar da ke damunsu ne suka iya bincike?”
A cikin wata sanarwa, kakakin rundunar Manjo-Janar Edward Buba ya ce duk da yake ‘yan Najeriya na da ‘yancin gudanar da zanga-zangar lumana, to amma zanga-zangar da aka shata somawa a ranar 1 ga watan Agusta kan iya rikidewa zuwa tarzoma da tashin hankali, kamar yadda lamarin ya auku a kasar Kenya.
Wannan taro na gudana ne a fadar gwamnatin tarayyar Najeriya dake Abuja.
Ma’aikata 5 sun mutu lokacin da wani ginin da ba’a kammala ba ya ruguje akan titin Wilson Mba, a rukunin gidaje na Arowojobe, dake unguwar Maryland, ta jihar Legas da safiyar yau Alhamis.
Hakan na kunshe ne a cikin sanarwar da aka fitar bayan kammala taron kungiyar gwamnonin wanda aka soma a daren jiya Laraba aka kuma kammala da safiyar yau Alhamis a birnin Abuja.
Domin Kari
No media source currently available