A jiya Lahadi, wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne suka afkawa caji ofis din Jakana dake karamar hukumar Konduga ta jihar Borno, inda suka hallaka wani direban ‘yan sanda da wata mata.
Haka kuma ‘yan ta’addar sun cinnawa wasu motocin sintirin jami’an ‘yan sandan da na ‘yan sa kan “Civilian JTF 2 da babur guda wuta, tare da yin awon gaba da wasu bindigogi da albarusai a harin da suka kai.
Garin Jakana mai nisan kilomita 35 daga kan babbar hanyar Maiduguri zuwa Damaturu ya kasance hanyar da ‘yan ta’addar suka jima suna amfani da ita tsawon lokaci.
Majiyoyi a garin na jakana sun bayyana cewar ‘yan ta’addar sun afkawa caji ofis din ne da misalin karfe dayan dare tare da yin musayar wuta da jami’an tsaro tsawon sa’o’i gabanin su arce bayan sa’a 2.
A wata hira ta wayar tarho da gidan talabijin ta Channels, Shugaban karamar hukumar Konduga, Abbas Ali Abari, ya tabbatar da afkuwar lamarin sai dai ya ce bashi da adadin wadanda al’amarin ya rutsa dasu.
A cewarsa, “na samu kiran gaggawar cewar mayakan Boko Haram sun afkawa caji ofis din Jakana a daren jiya. Yanzu ina tattaunawa da baturen ‘yan sandan, amma duk lokacin da na samu cikakken bayani akan lamarin zan shaida muku.”
Duk kokarin jin ta bakin kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Kenneth Daso a yayin hada wannan rahoto ya ci tura.
Dandalin Mu Tattauna