A sakon daya wallafa a shafinsa na X a yau Talata, Kyari, ya bukaci shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote, ya fito fili ya bayyana sunan jami’in NNPC daya mallaki masana’antar tace albarkatun man fetur a kasar Malta.
Majalisar ta amince da dokar ne ranar Talata bayan da Shugaban Najeriya, Bola Tinubu ya aika kudirin doka kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa zuwa Majalisar domin amincewa da shi.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya aika kudirin doka kan sabon mafi karancin albashin ma’aikata na kasa zuwa majalisar dokokin kasar domin amincewa da shi.
Mabiya Addinin Kirista Iklisiyyar United Methodist Church a Najeriya, sun gudanar da zanga zanga ta lumana don nuna kyama ga batun auren jinsi da wassu Shugabannin Iklisiyar Methodist Church ke kokarin ganin mabiyan sun amince dashi.
Kwararru a fannin siyasa da gudanar da mulki a Najeriya sun bayyana ra'ayoyi mabanbanta kan janyewa daga tsayawa takara da shugaba Joe Biden ya yi, inda wasu ke gani ya yi abin da wasu kasashe za su yi koyi da shi.
Kotun Daukaka Kara dake zamanta a Legas ta tabbatar da hukuncin kisa akan wani dan asalin denmark, Peter Nielsen, wanda aka yankewa hukuncin kisa a shekarar 2022 saboda hallaka matarsa ‘yar Najeriya, Zainab da diyarsu, Petra.
A yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce a game da ingancin man dizal da matatar man Dangote ke fitarwa inda wasu ke ganin akwai masu son ganin bayan kamfanin, hukumar kula da dokokin fannin man fetur ta NMDPRA ta sake jaddada cewa ba haka abin ya ke ba.
Gwamnatin jihar Katsina ta bullo da dokar zaman Iddah ga mata ma’aikatan gwamnati tsawon watanni hudu da kwana goma idan sun rasa mazajensu.
Batun halalci ko haram na gudanar da zanga-zanga don kalubalantar salon mulkin shugabanni ya janyo sabanin fahimta tsakanin malaman addinin Islama a Najeriya.
Hukumar kula da makamashi ta duniya ta IEA, ta kiyasta cewa mutane miliyan 600 a Afrika basu da wutar lantarki. Duk da cewa Najeriya ta sami lantarki sama da karni guda da ya wuce, har yanzu ba a samun igantacciyar wutar lantarki a kasar. Amma wani dan Najeriya ya fito da wata sabuwar fasaha.
Gwamnatin Najeriya ta sanar da cin kamfanin Meta tarar dala miliyan 220, inda ta ce binciken da ta gudanar ya gano an saba dokokin kare bayanai na kasar lokuta da yawa a shafukan Facebook da WhatsApp.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.