Babu wata kungiya da ta dauki alhakin harin na ranar Laraba, amma kungiyar masu ikirarin jihadi ta Boko Haram kan kai ire-iren wadannan hare-hare.
Bayanai daga jihar Nejan Najeriya na nuna cewa kimanin mutane 8 suka mutu a zanga-zangar adawa da matsalar yunwa da tsadar rayuwa da ta barke a ranar Alhamis a sassan kasar
Wasu ‘yan Najeriyar mazauna wasu kasashe da ke bibiyar al’amuran da ke gudana a kasar da dama sun yarda cewa matsin rayuwar da jama’ar kasar ke fama da ita, wani abin tashin hankali ne da aka jima ba a duba wa ba.
'Yan sanda sun yi ta harba barkonon tsohuwa domin tarwatsa masu zanga zangar tsadar rayuwa a shataletalen kofar shiga anguwan Lekki, a jihar Legas, inda aka yi zanga zangar #Endsars a baya.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka fita dandalin zuwa Eagle Square sun fadawa Muryar Amurka cewa matakin jefa musu barkonon tsohuwa ba zai dakile su ba.
Gwamnan ya ce majalisar tsaro ta jihar Kano ta amince da wannan mataki kuma dokar ta fara aiki nan take.
Matasa a sassan Najeriya sun fara gudanar da zanga zanga kan tsadar rayuwa da sauran matsaloli da suke addabar kasar.
Rokon na zuwa ne bayan da Majalisar Dattawan ta sake hallara bayan wata ganawar sirrin da ta shafe kusan sa’o’i biyu a yau Laraba.
Hukumar zaben jihar Kano mai zaman kanta (KANSIEC) ta sanar da cewa za ta gudanar da zabubbukan kananan hukumomi a ranar 30 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Asusun Rancen Karatun Daliban Najeriya (NELFUND) ta bayyana cewa za ta biya naira milIyan 850 ga manyan makarantu a matsayin kudin makaranta a yau laraba.
A yau Laraba, sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Sanata George Akume, ya yi kira ga ‘yan Najeriya a kan kada su shiga cikin zanga-zangar gama garin da aka tsara yi a kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar.
Domin Kari
No media source currently available