Ministan yace an cimma wannan matsaya ne a yayin wata ganawa tsakanin Shugaban Najeriya, Bola Tinubu da shugabannin kungiyoyin kwadago na NLC da TUC a Abuja a yau Alhamis.
A yayin wata zanga-zangar lumana a birnin tarayya Abuja, jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da DSS sun rufe mambobin kungiyoyin SSANU, NASU da JAC sun hana su tattakin mika koken su cikin wasika ga gwamnatin tarayya ta hannun ma’aikatun ilimi da na kwadago.
Kasa da mako guda da Sanata Mohammed Ali Ndume ya caccaki yadda ake gudanar da mulki a gwamnatin Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, Majalisar Dattawa ta bi umurnin Jamiyyar APC, ta tsige shi daga mukamin babban Mai tsawatarwa, tare da maye gurbin sa da Sanata Tahir Monguno.
Bukatar Shugaba Tinubun na kunshe ne a cikin wasikar daya aikewa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, wacce aka karanta a zauren majalisar a yau Laraba.
A yau Laraba, Majalisar Dattawan Najeriya ta sanar da cire Sanata Ali Ndume daga kan mukaminsa .
Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nada sababbin Sarakuna masu daraja ta biyu a masarautun Karaye, Rano da kuma Gaya.
Bayan shafe kwananki 20 a hannun yan bindiga, Hajiya Hauwa’u Adamu mahaifiyar mawakin Najeriya Dauda Kahutu Rarara da aka fi sani da Rarara ta samu kubuta da saduwa da ‘danta.
Yan Nigeria na ci gaba da maida martani akan matakin da gwamnatin kasar ta dauka na raba tireloli ashirin -ashirin na kayan abinci ga kowacce jiha da ke fadin kasar,
Hukumar kididdiga ta kasa NBS, ta bayyana cewa, kayayyakin amfanin yau da kullum na cigaba da hauhawa a Najeriya babu ƙakkautawa inda farashin kayayyakin masarufi ya tashi da kaso 11.34 % idan aka kwatanta da farashinsa a shekarar da ta gabata.
Gwamana Abba Kabir Yusuf ya rattaba hannu kan kudirin dokar kafa masarautu ta bana da Majalisar Dokokin jihar ta zartar.
Babban likitan Alhazan Dokta Abubakar Adamu Isma’il ya yi bayanin alkaluman da aka tattara bayan kammala aikin hajjin na wadanda a ka rasa inda ya tabbatar cewa “jimilla gaba daya in ka hada da Madina da Makkah da Masha’ir mutum 15 kenan.
Domin Kari
No media source currently available
A jawabin da ya gabatar, shugaban kasar, Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da kuma ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne adaidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa.
Mataimakan ‘yan takarar shugaban kasa, Tim Walz na jam’iyyar Democrat da kuma JD Vance na Republican sun fafata a muhawarar su ta farko wacce kuma ita ce kadai da za su yi kafin zaben shugaban kasa a watan Nuwamba. Ga fasaarar rahoton Tina Trinh daga New York.
A bana, sau biyu ana yin yunkurin halaka dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Republican Donal Trump. Muryar Amurka ta ji ta bakin wasu Amurka da suka mallaki bindiga wadanda suka ce yunkurin halaka Trump din bai sauya matsayarsu ba a game day dokokin mallakar bindiga a Amurka.