Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hajjin Bana: Yadda Hukumar NAHCON Ta Kashe Tallafin N90bn


Shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi
Shugaban Hukumar NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi

A yayin aikin hajji na bana dai, hukumar NAHCON ta kayyade kudin da maniyatta za su biya a kan dala dubu 5 da 692.25 a madadin wanda aka tsara a farko-farko na dala dubu 6 da 401.31 inda aka sami ragin dala 700 da centi 6 a bisa ana canjin naira zuwa dala a kan naira 456 a waccan lokaci.

A yayin da ake ci gaba da tafka muhawara akan cewa ko ya dace gwamnati ta rika bada tallafi don baiwa ‘yan Najeriya rangwame a kan kujerar aikin Hajj na Musulmai ko zuwa kasa mai tsarki da mabiya addinin Kirista ke yi, Hukumar alhazai ta Najeriya wato NAHCON ta fitar da bayani a kan yadda ta kashe tallafin naira biliyan 90 da gwamnatin tarayyar Najeriya ta ba ta a lokacin aikin hajjin bana.

A yayin aikin hajji na bana dai, hukumar NAHCON ta kayyade kudin da maniyatta za su biya a kan dala dubu 5 da 692.25 a madadin wanda aka tsara a farko-farko na dala dubu 6 da 401.31 inda aka sami ragin dala 700 da centi 6 a bisa ana canjin naira zuwa dala a kan naira 456 a waccan lokaci.

A yadda aka kiyasta tun farko, maniyyaci zai biya kudin kujera dala dubu 5 da 192.25, kudin guzirin tafiya na BTA dala 500, canjin dala a kasuwannin bayan fagge, naira 1474 da digo 615 kwatankwacin naira miliyan 8 da dubu 393 da doriya.

Ita kuma hukumar NAHCON tsara za’a sami dala a kan naira 850 wanda ke nufin a wannan lissafin za’a sami naira miliyan 4 da dubu 838 da doriya sai aka sami rarar naira miliyan 3 da dubu 555 da doriya sakamakon sabanin da aka samu wajen canjin kudi.

Daga bisani gwamnatin tarayyar Najeriya ta bada tallafin naira biliyan 90 wanda a lokacin maniyyata da suka biya kudin kujerar su a matakin jihohi sun kai 48, 414.

A bisa wannan tallafin, kowanne maniyaci zai samu naira miliyan 1 da dubu 637 da doriya tare da biyan naira miliyan 1 da dubu 918 da doriya a matsayin gibin da aka samu duk kuwa da tallafin gwamnatin tarayya.

Wannan dai na nufin cewa, tun farko hukumar Alhazai na Najeriya ya fuskanci kalubale da dama sakamakon rashin biyan kudin kujerun da wuri da maniyyata ba su yi ba a lokacin.

A yanzu dai hukumar NAHCON ta ce ta fara shirye-shirye kan gudanar da aikin hajj na badi wato shekarar 2025 tun ranar 16 ga watan Yunin da ya gabata jim kadan bayan da hukumar kula da aikin hajj na kasar Saudiyya ta fara nata shirye-shiryen.

Ku saurari bayani cikin sauti daga bakin shugaban hukumar NAHCON, Malam Jalal Ahmad Arabi.

Hajjin Bana: Yadda Hukumar NAHCON Ta Kashe Tallafin N90bn
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG