Rokon na zuwa ne bayan da Majalisar Dattawan ta sake hallara bayan wata ganawar sirrin da ta shafe kusan sa’o’i biyu a yau Laraba.
Hukumar zaben jihar Kano mai zaman kanta (KANSIEC) ta sanar da cewa za ta gudanar da zabubbukan kananan hukumomi a ranar 30 ga watan Nuwamba mai zuwa.
Asusun Rancen Karatun Daliban Najeriya (NELFUND) ta bayyana cewa za ta biya naira milIyan 850 ga manyan makarantu a matsayin kudin makaranta a yau laraba.
A yau Laraba, sakataren gwamnatin tarayyar Najeriya, Sanata George Akume, ya yi kira ga ‘yan Najeriya a kan kada su shiga cikin zanga-zangar gama garin da aka tsara yi a kan tabarbarewar tattalin arzikin kasar.
Kwamitin zai samar da tsarin da za’a yi amfani da shi wajen aiwatar da biyan mafi karancin albashin ba tare da bata lokaci ba.
Fitacciyar mawakiyar nan ‘yar Najeriya Onyeka Onwenu ta rasu a asibitin Reddington da ke Legas bayan da ta yanke jiki ta fadi a wajen wani bukin murnar zagayowar shekarar haihuwa.
Wani jami’i ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar, a yau Talata kasar Libya ta mayar da bakin haure 369 zuwa kasashensu na asali; Najeriya da Mali ciki harda mata da yara kanana fiye da 100
Shugaban Hukumar kula da Gidajen Yarin Najeriya, Hailey Nababa ne yayi wannan gargadi a sanarwar daya fitar yau Talata a Abuja.
Kamfanin ya wallafa a shafinsa na X cewa, “Muna sanar wa abokan hulda cewa zamu rufe ofisoshinmu dake fadin Najeriya a yau, 30 ga watan Yulin 2024.”
A cewar Muhammad Idris, matakin na cikin jerin matakan da gwamnatin Shugaba Tinubun ke dauka na saukaka rayuwar ‘yan Najeriya.
Binciken da rundunar ‘yan sandan kasa da kasa (INTERPOL) ta gudanar ya nuna cewa duk bayan sa’a guda, ana fitar da dubban daruruwan dalolin haramun daga Najeriya zuwa sauran sassan duniya.
Domin Kari
No media source currently available