Tsohon hafsan mayakan ruwa, Admiral Allison Madueke mai ritaya wanda kuma ya yi gwamna a jihohin Anambra da Imo ya bukaci kotu ta umarci tsohuwar Minister Diezani Allison- Madueke ta daina amfani da sunan shi, ta koma amfani da sunan mahaifinta Agama domin daina bata mashi suna.
Jakadiyar Tarayyar Turai a Najeriya da Kungiyar Raya Kasashen Afrika ta Yamma (ECOWAS), Samuela Isopi, ce ta bayyana hakan a yayin taron bunkasa kasuwanci tsakanin Najeriya da kungiyar kasashen Turai (EU) karo na 9 da ya gudana a Abuja a yau Talata.
‘Yan bindiga sun hallaka wani malami a jami’ar tarayya ta Dutsin-Ma dake jihar Katsina.
Jami’an hukumar bada agajin gaggawan sun dora alhakin faruwar lamarin akan dan kwangilar, saboda bijirewa umarnin da Hukumar Kula da Gine-Gine ta birnin Abuja ta bashi na ya dakatar da aiki.
Masana sun bayyana mata da ke kai harin kunar bakin wake a matsayin makaman ‘yan ta’adda na boye, kasancewa ba a zaton za su iya kai irin wannan harin.
“Duba da cewa jirgi ne mara matuki, ba a samu wani da ya mutu ko ya ji rauni ba.” In ji wata sanarwa da darektan yada labarai, Air Vice marshal Edward Gabkwet ya wallafa a shafin Facebook na rundunar.
Gwamnatin jihar Legas ta kuma ba da sanarwar samun gagarumar raguwar yawan mutanen da ke kamuwa da kwalarar a kowace rana.
A cewar Kwamandan Shiyyar Kano na Hukumar FRSC, “binciken farko ya nuna akwai yiyuwar cewar tsananin gudu ne ya sa tirelar ta kwace daga hannun direbanta”.
Mai Shari’a Omotosho, yace Kanu ya gaza gabatar da gamsassun hujjojin da zasu tabbatar da ikirarinsa na hana shi ganawa da lauyoyinsa ba tare da tarnaki ba.
Domin Kari
No media source currently available