Umarnin kotu dake cin karo da juna sun haifar da dambarwa game da masarautar Kano inda Babbar Kotun Tarayya dake Kano ta bada umarnin fitar da sarki Muhammadu Sanusi na 2 daga gidan sarautar a yayin da ita ma Babbar Kotun Jihar Kano ta bada umarnin sauke sarki Aminu Ado Bayero Daga Kan Gadon Mulki.
Mai Shari’a Ariwoola wanda shine Shugaban Majalisar Harkokin Shari’ar Najeriya (NJC), yayi sammacin alkalan 2 zuwa wani taron gaggawa a ofishinsa a gobe Alhamis, 30 ga watan Mayun da muke ban kwana dashi.
Sanarwar da daraktan yada labaran NJC, Soji Oye, ya fitar tace taron, wanda zai kasance sharar fage ga cikakken binciken da NJC din ke shirin gabatarwa, zai baiwa alkalin alkalan damar sauraron bayanan alkalan 2 game da dambarwar Kano mai tada hankali da kuma hukunce-hukunce masu cin karo da juna da suka rika fitowa daga kotuna game da masarautar Kano.
Akwai alamun masu karfi dake nuna cewar Majalisar Harkokin Shari’ar Najeriya zata gudanar da taron gaggawa a mako mai zuwa inda ake sa ran gayyatar alkalan da al’amarin ya shafa tare da gudanar da bincike akansu.
Dandalin Mu Tattauna