Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Zartar Da Kudirin Komawa Kan Tsohon Taken Najeriya


Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)
Zauren majalisar dattawan Najeriya (Facebook/Nigerian Senate)

Kudirin, wanda cikin hanzari ya tsallake karatu na 1 dana 2 a Alhamis din data gabata, yanzu haka yana dakon sa hannun Shugaba Bola Tinubu domin zama doka.

Majalisar Dattawan Najeriya ta zartar da kudirin taken kasa na shekarar 2024 domin komawa kan tsohon taken daya soma da kalmomin "Nigeria we hail thee " a turance.

Kudirin, wanda cikin hanzari ya tsallake karatu na 1 dana 2 a Alhamis din data gabata, yanzu haka yana dakon sa hannun Shugaba Bola Tinubu domin zama doka.

Majalisar Dattawan ta zartar da kudirin sauya taken kasa daga wanda ya soma daga "Arise o' compatriots" zuwa wanda ya fara da "Nigeria we hail thee".

Wani daga cikin shugabanin Majalisar Dattawan, Opeyemi Bamidele ya jaddada irin tasirin da taken ke dashi inda yace "da an kada shi yana karawa 'yan Najeriya kishin kasa. Wadanda suke raye a wancan zamani zasu iya tuna tasirin taken a tarihin Najeriya, inda yake dawo da dadadan tunanin shekarun farko-farko na zamanmu 'yantacciyar kasa".

A Litinin din da ta gabata, Majalisar Dattawan ta kaddamar da zaman sauraron ra'ayin jama'a game da taken Najeriya da al'amuran dake da alaka da shi.

Bamidele, wanda ya wakilci Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio, a zaman sauraron ra'ayin jama'ar, yace shedara ta 2 ta taken Najeriyar da ake amfani dashi a halin yanzu zata kasance addu'a ga kasa.

Tsohon taken da aka kirkira lokacin da Najeriya ta samu 'yancin kai a ranar 1 ga watan Oktoban 1960 zai maye gurbin wanda ake amfani dashi a halin yanzu.

Manufar kudirin shine sake farfado da tsohon taken da aka yi watsi dashi a 1978 lokacin gwamnatin mulkin sojan Olusegun Obasanjo.

Wani bakon haure dan asalin Burtaniya daya zauna a Najeriya mai suna Jean Williams ne ya rubuta taken na "Nigeria we hail thee " .

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG