ABUJA, NIGERIA - Da ya ke bahasi kan lamarin, gwamnan jihar Gombe wanda shine shugaban kungiyar gwamnonin Arewa Muhammadu Inuwa Yahaya ya ce tun kaddamar da rijiyoyin a Agustar 2022 ba ya jin wani ya sake taka kafar sa don duba aikin.
Gwamna Yahaya ya kara da cewa rashin tsayin daka ya jawo yankin Arewa na kwana kan dami ba cin gajiya kamar kaza da ba ta san dawar gari ba.
Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kaddamar da rijiyoyin da nuna hakan zai zaburar da kamfanin mai na NNPC kan ci gaba da aikin nemo mai a Anambra, Dahomey, Sokoto, Binuwai, yankin tafkin Chadi da kuma maremarin Bidda.
A lokacin shugaba Buhari wanda ya bugi kirji cewa, gwamnatin sa ta tada aikin da ya gagari kundila na gano mai a Arewa, ya sanar da cewa, sun samar da danyen fetur fiye da ganga biliyan daya da ma'aunin iskar gas fiye da biliyan 500.
Yayin da sarakuna da sauran jama'ar yankin Arewa ke annashuwar samun mai a taron, Shugaban kamfanin NNPC Mele Kyari ya ce wannan kafin alkalamin arziki ne. Bisa ga cewarsa, "Wannan gano man ya kara sanya fahimtar arzikin fetur a sassan Najeriya, da zummar karo gano tarin arzikin man." ]
Saurari cikakken rahoton:
Dandalin Mu Tattauna