Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya: Dattawan Arewa Sun Koka Kan Matsalar Bacewar Yara A Yankin


Taron Kungiyar Tuntuba Ta Dattawan Arewa ACF
Taron Kungiyar Tuntuba Ta Dattawan Arewa ACF

Kungiyar tuntuba ta dattawan Arewa ACF, ta koka kan yadda ba’a zartar da hukuncin da ya kamata kan mutanen da ke da hannu akan matsalolin satar yara da akan yi safarar su daga yankin arewacin Najeriya zuwa kudanci domin sayar da su.

A yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Kano, kungiyar ta bukaci manyan joji-joji na jihohin Najeriya, musamman na yankin arewacin kasar da su kara kaimi wajen ganin doka tayi aiki akan mutane dake satar yara kanana su sayar dasu a yankin kudanci, bayan sauya musu addini da kuma suna.

Shugaban shugaban kungiyar ta ACF a Kano, Dr Goni Umar Farouk, ya ce “Makasudun wannan taro shine saboda ‘yan sanda da suka bada labari wasu yara da aka sato su daga Bauchi, aka kawo su Kano aka hada baki da wasu masu Unguwanni aka canza musu takardar haihuwa."

"Da ma a baya can an dade ana yin haka, akwai yara da yawa da aka sace daga arewa aka yi safarar su zuwa kudancin Najeriya domin sayarwa," a cewar Dr Farouk.

Hajiya A’ishatu Mai-Jama’a da ke wakiltar mata a kungiyar ta ACF, bayan nuna damuwar mata dangane da wannan al’amari ta fayyace mataki na ga gaba da suke shirin dauka.

Taron Kungiyar Tuntuba Ta Dattawan Arewa ACF
Taron Kungiyar Tuntuba Ta Dattawan Arewa ACF

Hajiya A’ishatu ta ce “Mataki na gaba dai shine mun turawa gwamnati kuma su-ma shugabannin al’uma mun gana da su kuma mun nusar da su abin da ya kamata su yi, kana zamu yi taro da ‘yan majalisun akan wannan batu”.

Taron dai ya kunshi sarakunan gargajiya na Igbo a Kano da Benin da kuma takwaran su na Yarabawa mazauna Kano, inda har-ma basaraken na Igbo Chief Efeanyi ke cewa, “wannan magana ta satar yara tana damun mu matuka, ba ma jin dadi, lallai ya kamata mu hada karfi da karfe domin kawar da wannan matsala.”

A nata bangaren, masarautar Kano ta ce wani lokaci a nan gaba zata tashi wata tawaga, domin ganawa da Sarakunan yankin Igbo a can kudancin Najeriya, a cewar wakilin Sarakin Kano a wurin taron Alhaji Shehu Mohammed, Sarkin Shanun Kano.

A baya bayan nan dai matasa a Kano sun so yin zanga-zangar lumana, domin nuna kin jinin wannan ta’ada ta sace yara a arewacin kasar domin sayar dasu a kudanci, amma dattawan garin suka dakatar dasu.

Saurari cikakken rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG