Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Fafaroma Francis Ya Yi Allah Wadai Da Hare-Haren Jihar Filato Da Wasu Abubuwa Da Ke Faruwa A Duniya


Fafaroma Francis
Fafaroma Francis

A wani martani mai ratsa zuciya da ya yi dangane da mummunar asarar rayuka da aka yi a jajibirin Kirsimeti a Najeriya, Fafaroma Francis ya mika addu’o’i da ta’aziyya ga iyalan da wani mummunan hari da aka kai jihar Filato ya rutsa da su.

Fafaroma ya roki Allah ya kubutar da Najeriya daga bala’in da ake yi na hallaka rayuka da 'yan bindiga ke yi ba kakkautawa.

Sama da mutane 160 ne wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kashe a kauyuka da dama na kananan hukumomin Mangu, Barkin Ladi da Bokkos na jihar, a daidai lokacin da duniya ke bukukuwan kirsimati, lamarin da ya tada hankalin duniya.

Bayan isar da sakonsa na Angelus na yau da kullun a ranar Lahadi, Paparoma ya mayar da hankalinsa ga tashe-tashen hankula na baya-bayan nan.

“Abin takaici, bikin Kirsimati a Najeriya ya fuskanci munanan tashe-tashen hankula a jihar Filato, inda aka kashe mutane da dama.

"Ina yi musu addu'a da iyalansu. Allah ya kubutar da Nijeriya daga wannan ta’asa!” a cewar fafaroma.

A wani mataki na nuna damuwarsa kan abubuwan dake faruwa a duniya, Fafaroma Francis ya kuma tuna da wasu da ke fuskantar matsaloli a sauran sassan duniya, ciki har da wadanda suka mutu sakamakon fashewar wata motar tanka a Laberiya da kuma wadanda suka fada cikin mawuyacin hali na yaki a Ukraine, Falasdinu, Isra'ila, Sudan, da Rohingya, da dai sauransu.

“A ƙarshen shekara, bari mu tambayi kanmu: Mutane nawa ne rikicin makami ya daidaita? Nawa ne suka mutu? Kuma nawa ne suka halaka, ke cikin wahala, da talauci?”.

Fafaroman ya bukaci masu ruwa da tsaki a yankunan da rikice-rikicen ke aukuwa da su yi biyayya ga lamirinsu, kuma su yi la'akari da irin wahalar da mutane ke ciki.

Kafin jawabinsa mai ratsa jiki kan tashin hankalin na baya-bayan nan, Fafaroma Francis ya yi magana game da inganta rayuwar iyali, inda ya kwatanta gwagwarmayar dangin Yesu Kiristi a duniya, da kuma yadda wassu ke fuskantar rikici a yau.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG